NNPP: Jam'iyyar Kwankwaso Ta Buɗe Kofa, Za a Yi Wa Tinubu Taron Dangi a 2027

NNPP: Jam'iyyar Kwankwaso Ta Buɗe Kofa, Za a Yi Wa Tinubu Taron Dangi a 2027

  • Jam'iyyar NNPP ta ce ƙofofinta a hude suke ga dukkan jam'iyyun da suke son haɗa maja da ita domin kawo karshen mulkin APC a 2027
  • Shugaban NNPP na ƙasa, Ajuji Ahmed ne ya bayyana hakan a wurin taron kaddamar da yakin neman zaben ɗan takarar gwamna a Ondo
  • Ya buƙaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa watau INEC ta ba kowace jam'iyya dama a zaɓen da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ondo - Jam'iyyar NNPP ta bayyana cewa a shirye take ta ƙulla ƙawance da sauran jam'iyyun siyasa a ƙasar nan domin kifar da APC a babban zaɓen 2027.

Shugaban NNPP na kasa, Dakta Ajuji Ahmed ne ya sanar da hakan a wurin kaddamar da kamfen ɗan takarar jam'iyyar a zaben gwamnan jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: NNPP ta zargi APC da rura wutar rikici a sauran jam'iyyu

Tambarin NNPP da Kwankwaso.
Jam'iyyar NNPP ta ce a shirye take ta haɗa maja domin kayar da APC a zaɓen 2027 Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Ajuji Ahmed ya yi ikirarin cewa APC na yin duk da mai yiwuwa don ta sake samun nasara a babban zaɓen 2027 mai zuwa, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2027: Ya kamata yan adawa ta tashi tsaye

A cewarsa, APC ta daɗe tana rura wutar rikici a tsakanin ƴaƴan jam'iyyun adawa domin kawai ta raba kawunansu ta yadda ba za su kai labari ba a zaɓe.

"APC na yin duk mai yiwuwa domin ganin ta lashe zaben 2027, muna da shaidar ita ke tada rikici a jam'iyyun adawa, saboda haka ya kamata mu farka.
"Ya kamata APC ta fara shirin barin gadon mulki bayan ƙarewar wa'adin Tinubu. NNPP ta fara haɗa kai da nufin ƙulla kawance da jam'iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.
"Don haka, kofofinmu a bude suke ta yadda idan har za a haɗa maja ta jam’iyyun siyasa, a shirye muke mu yi hakan.”

Kara karanta wannan

"Har yanzu yana jin raɗaɗin 2023," Jigon PDP ya kwancewa tsohon gwamna zani a kasuwa

- Ajuji Ahmed.

NNPP ta fara kamfe a jihar Ondo

Dangane da batun zaɓen gwamnan Ondo da za a yi a watan Nuwamba, shugaban NNPP ya roki hukumar zaɓe INEC ta ba kowace jam'iyya dama ba tare da nuna wariya ba.

Ya kuma yi kira ga al'ummar jihar Ondo su fito kwansu da kwarkata su zaɓi ɗan takarar jam'iyyar NNPP a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2024.

NNPP ta haskawa Tinubu hanyar ceto Najeriya

A wani rahoton kuma jam'iyyar NNPP ta samo mafita ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan taɓarɓarewar da tattalin arziƙin ƙasar nan ya yi.

NNPP ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya nemi taimakon tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan kan halin da ƙasar nan ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262