Rikici Ya Barke a APC kan Korar Ministan Tinubu, Shugabanni Sun Rabu Gida 2

Rikici Ya Barke a APC kan Korar Ministan Tinubu, Shugabanni Sun Rabu Gida 2

  • Rikicin jam'iyya ya barke a tsakanin shugabannin APC kan korar karamin ministan man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri
  • Shugabannin APC a yankin Kudu maso Kudu sun ce hassada da bakin ciki ne suka jawo korar ministan kuma lamarin ya saba doka
  • A makon da ya wuce ne shugabannin APC a jihar Bayelsa suka fitar da sanarwar korar Sanata Heineken Lokpobiri daga jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bayelsa - Shugabannin APC a Kudu maso Kudu sun rabu gida biyu kan ministan man fetur, Heineken Lokpobiri.

Shugabannin yankin Kudu maso Kudu sun yi zargin cewa hassada ce ta sanya aka kori Sanata Heineken Lokpobiri ba wani abu ba.

Kara karanta wannan

Da gaske alaka ta yi tsami tsakanin Majalisar Tarayya da Tinubu? an samu bayanai

Ganduje
Korar minista na ya tayar da kura a APC. Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Asali: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa shugabannin sun buƙaci waɗanda suka yi korar su kara duba kundin tsarin jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar APC ta kori ministan Tinubu

A makon da ya wuce ne shugabannin APC a jihar Bayelsa suka sanar da korar ministan man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri.

Punch ta wallafa cewa shugabannin APC a kananan hukumomin Ijaw ta Kudu da Ekeremor ne suka sanar da korar ministan daga jam'iyyar.

An yi martani ga shugabannin APC

Bayan korar Sanata Heineken Lokpobiri, shugabannin APC a Kudu maso Kudu sun ce sun yi watsi da matakin da kananan hukumomin suka dauka.

Lauyan APC a Kudu maso Kudu, Chukwuemeka Ogbuobodo ya ce kananan hukumomi ba su da izinin korar ministan. Ga abin da yake cewa:
Ya kamata su sake duba kundin mulkin APC domin duba yadda ake ɗaukar mataki a kan wanda ake zargi

Kara karanta wannan

Za a sasanta, kungiyar APC ta zubar da makamanta kan neman tsige Ganduje

Babu wanda ya ba shugabannin karamar hukumar damar korar ministan a tsarin jami'yyar APC.
Ya kamata waɗanda suka kori ministan su san cewa APC tana tafiya ne a kan doka da oda ba ra'ayin wasu ba.

- Chukwuemeka Ogbuobodo, Lauyan APC a Kudu maso Kudu

Hadarin Jigawa: Minista ya ce za a yi bincike

A wani labarin, Legit ta ruwaito cewa karamin ministan man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri ya ce za a yi bincike kan hadarin tankar mai a Jigawa.

A ranar Talata da dare aka yi hadarin inda a yanzu haka mutane sama da 150 sun kwanta dama sama da 100 kuma na kwance a asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng