Zaben 2027: NNPP Ta Zargi APC da Rura Wutar Rikici a Sauran Jam'iyyu

Zaben 2027: NNPP Ta Zargi APC da Rura Wutar Rikici a Sauran Jam'iyyu

  • Jam'iyyar NNPP ta dora alhakin rikice-rikicen jam'iyyun PDP, LP da ita kanta a kan APC gabanin babban zabe mai zuwa
  • Shugaban APC na kasa, Ajuji Ahmed ne ya bayyana haka, ya ce APC na daukar matakin ne domin ta samu nasara a 2027
  • Rikicin shugabanci ya rikita manyan jam'iyyun adawa a daidai lokacin da APC ta yi nasarar kashe wutar rikicin gidanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ondo - Jam'iyyar NNPP ta ce ta gano yadda jam'iyyar APC ke dauke da alhakin rura rikici a sauran jam'iyyun kasar nan saboda cimma bukatun kashin kai.

Kara karanta wannan

APC ta tsorata, ta janye daga fafatawa a zaben kananan hukumomi, ta fadi dalili

Shugaban NNPP na kasa, Ajuji Ahmed ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke kaddamar da takarar Olugbenga Edema gabanin zaben gwamnan Ondo a ranar Laraba a birnin Akure.

Jam'iyyu
NNPP ta zargi APC da haddasa rikici a jam'iyyu Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro shugaban na zargin jam'iyya mai mulki ta APC na da hannu a dukkanin rikicin da ake samu a sauran jam'iyyun kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An zargi APC da hannu a rikicin jam'iyyu

Shugaban jam'iyyar NNPP na kasa, Ajuji Ahmed ya zargi APC da shiga harkokin cikin gida na jam'iyyun adawa domin wargaza kan 'ya'yan jam'iyyun.

Ya ce APC na dabarar raunata karfin jam'iyyun domin ta samu saukin karbe ta daga hannun yan asalin cikinta saboda cimmana manufar kashin kai.

Ta ya rikicin jam'iyyu zai amfani APC?

Jam'iyyar adawa ta NNPP ta ce idan aka samu rikici da wargajewar sauran jam'iyyun adawa, haka zai ba APC damar nasara a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Tazarcen Tinubu: Yadda rikicin jam'iyyun PDP, LP da NNPP zai iya ba APC nasara a 2027

Shugaban NNPP na kasa, Ajuji Ahmed ya kara da cewa APC na yin makarkashiya ga sauran jam'iyyu, ta na haddasa rikici ta bayan gida a jam'iyyun

.

Rikicin jam'iyyu zai ba APC nasara?

A baya mun ruwaito cewa masana sun fara hasashen cewa rikicin cikin gida na jam'iyyun adawa da su ka hada da NNPP, PDP da LP zai iya ba APC nasara a kakar babban zaben 2027 mai zuwa.

A halin da ake ciki, ana samun rikicin shugabanci a jam'iyyar adawa ta PDP, LP da NNPP, yayin da ake zaton rigingimun za su iya shafar shirin jam'iyyun na tunkarar zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.