Jigon PDP Ya Bayyana Yadda Tinubu Ya Hana Shi Barin Najeriya
- Cif Olabode George ya bayyana dalilinsa na ƙin barin Najeriya bayan shugaba Bola Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa
- Tsohon mataimakin na shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa ya bayyana cewa haƙurin da aka ba shi ne ya sanya ya canza shawara
- Ya bayyana cewa da Bola Tinubu bai turo a ba shi haƙuri ba, da tuni ya fice daga cikin ƙasar nan yadda ya yi alƙawari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Cif Bode George, ya yi magana kan dalilinsa na ƙin barin Najeriya bayan Shugaba Bola Tinubu ya lashe zaɓe.
Bode George ya bayyana cewa da a ce Bola Tinubu bai turo shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajbiamila, ya lallashe shi ba, da tuni ya bar ƙasar nan.
Tsohon mataimakin shugaban na jam'iyyar PDP ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar talabijin ta Arise tv a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Yadda Tinubu ya lallaɓe ni", Bode George
Bode George ya bayyana cewa zuwan da Femi Gbajabiamila ya yi wajensa ne ya sanya ya canza shawara kan aniyarsa ta barin Najeriya.
A watan Janairun 2022, bayan da Tinubu ya bayyana aniyarsa ta yin takarar shugaban ƙasa, Bode George ya yi barazanar ficewa daga Najeriya idan har ya ci zaɓe.
"A lokacin yaƙin neman zaɓe na faɗi hakan kuma da gaske na ke cewa idan har Bola Tinubu ya yi nasarar lashe zaɓe, zan bar ƙasar nan."
"Suna jin hakan, sai Tinubu ya turo shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa wanda ƙanina ne daga jihar Legas, Femi Gbajabiamila, domin ya ba ni baki."
"Ya zo ya ce mani maigidansa ya ce na kwantar da hankali na. Sun san sun yi mani laifi. Sun ce suna ba ni haƙuri."
- Bode George
Jagoran PDP ya jiƙawa Atiku aiki
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban PDP, Bode George ya ce dole Atiku Abubakar ya jira 2031 idan yana son sake neman zama shugaban ƙasa.
Cif Bode George ya bayyana cewa dole ne yankin Kudancin Najeriya ya ci gaba da mulkin ƙasar nan har zuwa shekarar 2031.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng