Gwamna Abba Ya Fice daga Kano Ana Tsaka da Rikicin Jam'iyyar NNPP

Gwamna Abba Ya Fice daga Kano Ana Tsaka da Rikicin Jam'iyyar NNPP

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shilla zuwa birnin tarayya Abuja a ranar Talata, 15 ga watan Oktoban 2024
  • Abba Kabir Yusuf ya fice daga jihar ne yayin da ake ci gaba da rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano
  • Ficewar gwamnan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, yake a cikin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fice daga jihar a ranar Talata, 15 ga watan Oktoban 2024.

Gwamna Abba Kabir ya bar jihar ne yayin da ake ci gaba da samun rikici a jam'iyyar NNPP mai mulki a Kano.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan rikicin NNPP a Kano, ya faɗi shawarar da ya yanke

Gwamna Abba ya bar Kano
Gwamna Abba Kabir ya fice daga Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Gwamna Abba ya jagoranci sasantawa tsakanin sakataren gwamnatin jihar (SSG), Abdullahi Baffa Bichi, da mambobin NNPP na mazaɓarsa bayan sun samu saɓani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya fice daga Kano

Gwamna Abba dai ya shafe kusan awanni biyu yana jira a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano kafin ya tashi zuwa babban birnin tarayya Abuja.

Abba Kabir Yusuf ya fice daga Kano ne a daidai lokacin da jagoran NNPP na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yake a jihar.

Kwankwaso ya gana da jiga-jigan NNPP

Kwankwaso dai ya gana da jiga-jigan jam’iyyar, shugaban majalisar dokoki, Jibril Falgore, da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa da masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomin jihar kan wasu batutuwan da ba a bayyana ba.

Hakan dai na zuwa ne bayan an samu ɓullar wata ƙungiya da ke neman Kwankwaso ya sakarwa Gwamna Abba mara wajen gudanar da mulkin Kano.

Kara karanta wannan

Yadda Abba ya kashe wata wutar rikicin da aka kunna masa a Kano

NNPP ta dakatar da jiga-jigai a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa rikici ya ƙara tsananta a jam'iyya mai-ci, NNPP ta dakatar da sakataren gwamnatin jiha, Abdullahi Baffa Bichi.

Haka nan kuma NNPP ta dakatar da kwamishinan sufuri na jihar Kano, Muhammad Diggol kan zargin rashin ladabi da biyayya ga jam'iyyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng