Tafiyar Kwankwasiyya Ta Gamu da Cikas, Sabon Shugaban NNPP Ya Bayyana a Kano
- Jam'iyyar NNPP ta tsunduma rikici bayan wasu daga cikin yan jam'iyyar sun balle daga tafiyar Kwankwasiyya
- Tsagin da ya bayyana Barista Dalhatu Shehu a matsayin shugaban jam'iyya ya zargi Rabi'u Musa Kwankwaso da son korarsu
- Barista Shehu ya shaidawa Legit cewa su ne su ka kafa jam'iyyar NNPP, kuma aron wuri kawai aka ba Kwankwaso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Rikici ya kara kunno kai a jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano yayin da aka samu bayyanar sabon shugaba a cikinta.
A ranar Talata ne daya daga cikin 'ya'yan NNPP a jihar, Dalhatu Shehu ya bayyana kansa a matsayin sabo kuma halastaccen shugaban jam'iyya.
Baristan ya shaidawa Legit cewa dama tun can tsaginsu ke jagorancin NNPP gabanin shigowar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar NNPP ta rabu a jihar Kano
A zantawarsa da Legit, Barista Dalhatu Shehu da ya bayyana kansa a matsayin sabon shugaban NNPC ya zargi Sanata Kwankwaso da korar wasu daga cikinsu.
"Mu ne yan jam'iyyar NNPP na asali, mu Kwankwaso ya zo ya tarar a cikin ita wannan jam'iyya. Aka ara masa wuri ya yi takara, saboda haka da ya samu nasara a Kano sai ya ke so ya mallake jam'iyyar ta zama tasa,"
- Barista Dalhatu Shehu.
Ya bayyana cewa daya daga korafinsu na daga cikin yadda Kwankwasiyya ta fitar da yan takarar zaben kananan hukumomi, kuma ya zargi hukumar zaben Kano da zama yar amshin shatan Kwankwasiyya.
"Ba mu da tsagi a NNPP," Dungurawa
Shugaban NNPP na Kano, Dr. Hashim Dungurawa ya bayyana mana cewa babu wani bangare ko tsagi a jam'iyyarsa.
Ya yi zargin wadanda ake cewa sun ja zuga dama ba yan jam'iyyar ba ne, ya ce sojojin haya ne kawai a NNPP.
Abba ya sasanta rikicin NNPP a Kano
A baya mun ruwaito cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya shiga tsakani wajen sasanta rikicin cikin gida ya ya balle tsakanin manyan kusoshin tafiyar NNPP.
An samu sabani ne tsakanin Sakataren gwamnatin Kano, Abdullahi Baffa Bichi da wasu yan jam'iyyar inda ake zarginsa da raba Abba da Rabi'u Musra Kwankwaso.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng