Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Tsohon Mataimakin Gwamna da Wasu Mutum 6

Jam'iyyar APC Ta Dakatar da Tsohon Mataimakin Gwamna da Wasu Mutum 6

  • APC ta ɗauki matakin ladabtarwa kan tsohon mataimakin gwamnan Bayelsa da wasu 'ya 'yan jam'iyyar da ake zargi da laifi
  • APC ta dakatar da Werinipre Seibarugu da wasu mutane shida har sai baba ta gani bisa zarginsu da yi wa jam'iyyar zagon ƙasa
  • Jam;iyyar ta ce ta ɗauki wannan matakin ne bayan ta samu rahoton kwamitin da ta kafa domin bincikar zargin da ake yi musu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bayelsa - Jam’iyyar APC reshen Bayelsa, ta dakatar da wani tsohon mataimakin gwamnan jihar, Werinipre Seibarugu da wasu har sai baba ta gani.

APC ta dakatar da mutanen ne a reshenta na ƙaramar hukumar Yenagoa ta jihar bisa zargin yi wa jam'iyyar zagon ƙasa.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun kamo hanyar warware rikicin da ya addabi jam'iyyar

APC ta dakatar da tsohon mataimakin gwamnan Bayelsa
Jam'iyyar APC ta dakatar da tsohon mataimakin gwamna a Bayelsa Hoto: Legit.ng
Asali: Original

APC ta dakatar da wasu mambobinta a Bayelsa

Jaridar The Punch ta ce Werinipre Seibarugu, wanda ya kasance tsohon mataimakin gwamna ya kuma taɓa riƙe muƙamin muƙaddashin gwamna da shugaban majalisar dokokin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Seibarugu ya kasance mataimakin gwamna ne ga tsohon ƙaramin ministan albarkatun man fetur kuma tsohon gwamnan Bayelsa, Cif Timipre Sylva.

Shugaban APC na ƙaramar hukumar Yenagoa, Mista Tonye Okokuro, ya sanar da dakatarwar da aka yi musu, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

Waɗanda aka dakatar tare da Seibarugu sun haɗa da Osomkime Blankson, Mista Alex Blankson sai kuma Cif Olomo Agbama Apina.

Sauran su ne: Dakt Pakinson Mamanuel, Ebiye Waripamo da Fasto Esther Saiyou.

Jam'iyyar APC ta same su da laifi

Okokuro ya shaida wa manema labarai cewa dakatarwar ta biyo bayan samun rahoton kwamitin binciken da aka kafa ne kan zarge-zargen yi wa jam'iyyar zagon ƙasa da ake yi musu.

Kara karanta wannan

Sukar Tinubu: Kalaman sanatan APC na neman kara sanya shi cikin matsala

A ƙarshen makon da ya gabata ne jam’iyyar APC ta dakatar da ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, da ɗan takarar gwamna a zaɓen 2019, Cif David Lyon da wasu mutane takwas.

Mambobin jam'iyyar APC sun koma NNPP

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai adawa a jihar Kano ta samu koma baya yayin da mambobinta suka sauya sheƙa zuwa NNPP.

Sama da mambobin jam’iyyar APC guda 1,000 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano da ke yankin Arewa maso Yamma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng