Sabon Shugaban Tsagin PDP Ya Shiga Ofis duk da Kotu ta Hana Taba Damagum

Sabon Shugaban Tsagin PDP Ya Shiga Ofis duk da Kotu ta Hana Taba Damagum

  • Tsagin PDP ta tabbatar da nada sabon shugaba, Yayari Mohammed da zai jagorance ta bayan rikici ya balle a jam'iyyar
  • A sanarwar da Yayari Mohammed ya fitar, ya bayyana cewa ya amince da nadin da aka yi masa kuma zai yi jagoranci bisa doka
  • Amma daya tsagin PDP ya shaidawa Legit babu bangare a cikinta, kuma doka ce ta tabbatar da nadin Ambasada Umar Damagum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Shugaban wani tsagin jam’iyyar PDP, Yayari Mohammed ya bayyana cewa ya kama aiki bayan tsagin kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya nada shi.

Yayari Mohammed ya bayyana haka ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke fama da rikicin gida da ya raba ta gida biyu.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta karo kayan aiki domin ragargaje yan ta'adda a Arewa

Jam'iyya
Sabon shugaban PDP ya fara aiki Hoto: Auwal Musa Muhammad Kaska
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa shugaban tsagin PDP ya bayyana fara aiki a wata sanarwar da ya fitar a babban birnin tarayya duk da umarnin kotu na dakatar da haka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayari ya amince da jagorancin tsagin PDP

Jaridar The Nation ta tattaro cewa Yayari Mohammed ya amince da zabarsa da tsagin PDP ya yi domin ya jagorance su bayan sun ware kansu daga jam’iyyar.

Yayari Mohammed ya yi alkawarin cewa za a tafiyar da jam’iyyar a karkashin doka da tsari kamar yadda ya ke a kundin dokokin PDP.

Jam'iyyar PDP ta ce babu rarrabuwar kai

Mataimakin sakataren yada labaran PDP na kasa, Barista Ibrahim Abdullahi ya shaidawa Legit cewa kan ‘ya’yan jam’iyyar a hade ya ke.

Ibrahim Abdullahi ya kuma doka ce ta tabbatar da shugabancin Umar Damagum.

Kara karanta wannan

Rikici ya turnuke PDP, tsohon Gwamna yana neman yi wa jam’iyyarsa dariya

Ya kara da cewa babu zancen rarrabuwar kai a cikin PDP, amma ya zargi wasu tsiraru a cikin jam’iyyar da karbo kwangilar kawo rikici.

Gwamnoni na shirin magance rikicin PDP

A baya mun wallafa cewa gwamnonin a karkashin jam'iyyar PDP za su zauna domin tattauna hanyar magance rikicin cikin gida da ya kunno kai cikinta, inda aka samu rabuwar kai.

Wannan na zuwa bayan kwamitin gudanarwar jam'iyyar ya rabu gida biyu, guda na goyon bayan Umar Damagum, guda kuma na marawa Yayari Mohammed baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.