2027: Tsohon Gwamnan PDP Ya Shawarci Atiku Ya Hakura da Takara, Ya Fadi Dalili

2027: Tsohon Gwamnan PDP Ya Shawarci Atiku Ya Hakura da Takara, Ya Fadi Dalili

  • Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi magana kan babban zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Ayo Fayose ya buƙaci Atiku Abubakar da ya haƙura da sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa
  • Tsohon gwamnan ya ce yanzu ƴan Najeriya sun fi son su samu ɗanyen jini wanda zai jagoranci ragamar ƙasar nan ba tsoho ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya ba ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, shawara.

Ayodele Fayose ya shawarci Atiku da ya haƙura da ci gaba da tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Fayose ya ba Atiku shawara
Ayo Fayose ya bukaci Atiku ya hakura da tsayawa takara Hoto: Ayo Fayose, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan na Ekiti ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar talabijin ta Channels tv kan rikicin da ya addabi PDP a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Sukar Tinubu: Kalaman sanatan APC na neman kara sanya shi cikin matsala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya yi rashin nasara a takarar shugaban ƙasa da ya yi a shekarun 1993, 2007, 2011, 2015, 2019, da 2023, inda ya faɗi sau uku a wajen zaɓen fidda gwani.

Ayo Fayose ya ba Atiku shawara

Fayose ya yi nuni da cewa bai kamata a zaɓe mai zuwa wanda ya kai shekara 80 ya yi sha'awar tsayawa takarar kujerar da ta fi kowace girma a ƙasar nan ba.

"Ina da tabbacin cewa a wannan matakin, tare da girmamawa a gare shi, ya kamata ya yi nesa da siyasar sake tsayawa takara."
"Zuwa lokacin da Shugaba Tinubu zai kammala, Atiku zai kai wajen shekara 80 ko 81, to menene abin sha'awa kuma?"
"Ya kamata mu koma gefe tun ana damawa da mu. Ina ganin girmansa sannan ina tunanin cewa ƴan Najeriya a yanzu fiye da kowane lokaci su na son ganin ɗanyen jini, to wane dalili zai sanya Atiku ya fito ya ce zai sake tsayawa takara."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dauki mataki bayan matashi ya cinnawa kakarsa wuta a Jigawa

- Ayodele Fayose

Atiku ya kawo gyara a tsarin mulki

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya buƙaci a yi sauyin tsarin mulki na shugaban kasa da gwamnoni.

Atiku Abubakar ya rubuta wasika ga majalisar tarayya domin ba shugaban kasa damar yin wa'adi ɗaya na shekaru shida kacal.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng