Gwamnonin PDP Sun Kamo Hanyar Warware Rikicin da Ya Addabi Jam'iyyar

Gwamnonin PDP Sun Kamo Hanyar Warware Rikicin da Ya Addabi Jam'iyyar

  • Gwamnonin jihohi PDP mai adawa a Najeriya za su gudanar da taro kan rikicin da ya daɗe yana addabar jam'iyyar
  • Taron gwamnonin zai lalubo hanyoyin magance rikicin jam'iyyar biyo bayan dakatar da wasu manyan jiga-jigai da aka yi
  • Gwamnonin za kuma su tattauna kan batun taƙaddamar da ake yi kan wanda ya kamata ya ci gaba da jan ragamar jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnonin PDP za su gudanar da wani taron gaggawa a yau biyo bayan dakatarwar da aka yi wa manyan jiga-jigan jam'iyyar a makon jiya.

Wani ɓangare na kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) da ke goyon bayan shugaban riƙo na ƙasa, Umar Damagum, ya dakatar da wasu jiga-jigan jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Sukar Tinubu: Kalaman sanatan APC na neman kara sanya shi cikin matsala

Gwamnonin PDP za su yi taro
Gwamnonin PDP za su yi taro domin warware rikicin jam'iyyar Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce majiya mai tushe ta shaida mata cewa taron gwamnonin jam’iyyar PDP na yau, zai nemo hanyoyin warware rikicin da ya addabi jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me gwamnonin PDP za su tattauna a kai?

Taron zai mayar da hankali musamman kan batun dakatarwar da aka yi wa jiga-jigan jam'iyyar.

An tattaro cewa gwamnonin za su kuma tattauna batun wanda zai maye gurbin Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Sannan kuma za su yi la’akari da kiran da jiga-jigan jam'iyyar daga yankin Arewa ta Tsakiya suke yi na yankin ya kammala wa'adin mulkin Iyorchia Ayu.

Wasu jiga-jigan PDP na son kujerar shugaba

Jaridar Thisday ta ce wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP daga yankin Arewa ta Tsakiya da suka haɗa da tsohon gwamnan Benue, Sanata Gabriel Suswam da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, tuni suka fara ƙoƙarin cike gurbin.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku ya gama bayanin yadda za a sasanta rikicin PDP, lissafi ya watse a ranar

Majiyoyi sun kuma bayyana cewa gwamnonin za su tattauna batutuwan da suka shafi taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) da ke tafe da kuma ɓangarorin da ake da su a cikin NWC.

Jam'iyyar PDP ta yi sabon shugaba a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP mai adawa ta zaɓi Yusuf Kibiya a matsayin sabon shugabanta na jihar Kano.

Rahotanni su ce Yusuf Kibiya ya yi nasara da gagarumin rinjaye inda ya samu kuri’u 3,964 yayin da ya doke abokin hamayyarsa Nura Nuhu wanda ya samu kuri’u 244.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng