Kano: PDP Ta Zabi Kwamishinan Kwankwaso a Matsayin sabon Shugaban Jam'iyya

Kano: PDP Ta Zabi Kwamishinan Kwankwaso a Matsayin sabon Shugaban Jam'iyya

  • A ranar Lahadi ne Halilu Mazagani ya bayyana sakamakon zaben shugabannin jam'iyyar PDP da aka gudanar a jihar Kano
  • Halilu wanda shi ne shugaban kwamitin zaben jam’iyyar, ya ayyana Yusuf Kibiya a matsayin sabon shugaban PDP na jihar
  • Yusuf Kibiya tsohon kwamishinan noma ne a zamanin tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, tsakanin 1999 zuwa 2003

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Rahotanni sun bayyana cewa PDP ta zabi Yusuf Kibiya a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na jihar Kano.

An ce Yusuf Kibiya ya yi nasara da gagarumin rinjaye inda ya samu kuri’u 3,964 yayin da ya doke abokin hamayyarsa Nura Nuhu wanda ya samu kuri’u 244.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku ya gama bayanin yadda za a sasanta rikicin PDP, lissafi ya watse a ranar

Jam'iyyar PDP ta zabi Yusuf Kibiya a matsayin shugabanta na jihar Kano
Kano: PDP ta zabi kwamishinan Kwankwaso, Yusuf Kibiya a matsayin shugabanta. Hoto: Kabiru Kibiyancy Hamisu
Asali: Facebook

Kano: PDP ta yi sabon shugaba

Yusuf Kibiya tsohon kwamishinan noma ne a zamanin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, tsakanin 1999 zuwa 2003, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kwamitin zaben jam’iyyar, Halilu Mazagani, ya sanar da nasarar Kibiya yayin da yake bayyana sakamakon zaben a ranar Lahadi.

"Yusuf Kibiya ya lashe zaben shugaban jam'iyyar bayan samun kuri'u 3,964 yayin da mai bi masa a baya Nura Nuhu ya samu kuri’u 244."

- A cewar cewar Halilu Mazagani.

"PDP za ta dinke barakarta" - Mazagani

Halilu Mazagani ya ce yadda zaben ya gudana lami lafiya manuniya ce cewa nan ba da jimawa ba jam’iyyar PDP za ta warware rikicin cikin gida da ke tsakanin wasu ‘ya’yanta.

JAridar New Telegraph ta rahoto shugaban jam'iyyar ya ce:

“Babu shakka jam’iyyarmu da ta kasance mafi girma a Afirka na fuskantar wasu kalubale na cikin gida, amma mun koyi yadda za mu zauna lafiya duk da bambance-bambancen mu.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP ya sake dagulewa, an nada sabon shugaban jam'iyyar, bayanai sun fito

“Ina tabbatar muku a yau cewa muna aiki tukuru domin tabbatar da hadin kai kuma muna yin gangami ba dare ba rana domin tabbatar da nasararmu a zaben 2027 mai gabatowa."

Shima da yake jawabi a wajen taron, tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bada tabbacin cewa jam’iyyar za ta yi nasara a zaben 2027.

Kano: 'Yan PDP sun koma APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu jiga jigan jam'iyyar PDP da ke gidan marigayi Ghali Umar Na'abba karkashin jagorancin Alhaji Ibrahim Tigaho sun sauya sheka.

An rahoto cewa tawagar masu sauya shekar a Kano sun sanar da ficewarsu daga PDP tare da shiga jam'iyyar APC ta hannun Sanata Barau Jibrin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.