Rikici Ya Turnuke PDP, Tsohon Gwamna Yana Neman Yi wa Jam’iyyarsa Dariya

Rikici Ya Turnuke PDP, Tsohon Gwamna Yana Neman Yi wa Jam’iyyarsa Dariya

  • A madadin a ji irinsu Ayodele Peter Fayose sun tashi tsaye domin kashe wuta rikicin PDP, sai aka ji akasin haka
  • Tsohon gwamnan ya yi dariya da ya ga yadda abubuwa suka cabewa PDP, ya ce za su zura idanu su sha kallo
  • Mutane sun yi tir da Ayo Fayose la’akari da yadda PDP ta yi masa riga da wando a siyasae Ekiti tun daga 2003

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Ana ta fama da rikici iri-iri a jam’iyyar hamayya ta PDP mai fatan a zaben 2023 ta karbe mulki daga hannun APC.

Wasu daga cikin wadanda suka kasance manya a jam’iyyar ta PDP a baya sun kauda idanu yayin da abubuwa suka rincabe.

Kara karanta wannan

Kanin tsohon gwamna ya ayyana kansa shugaban PDP, ya kori Atiku, Wike da sauransu

Ayo Fayose PDP
Tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose ya koma yi wa PDP dariya Hoto: @AyoFayose
Asali: Twitter

Ayo Fayose ya juyawa jam'iyyar PDP baya

Ayodele Peter Fayose ya na cikin wadanda aka gani ya fito a shafinsa na X ya na nuna babu abin da ya yi masa ciwo a rikicin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A maimakon a ji ya na neman yadda za a sulhunta, sai aka ci karo da Ayodele Fayose ya na cewa za su zurawa sarautar Allah ido.

"PDP: Abin ya koma kayataccen wasan kwaikwayo.
Bari mu zauna mu na kallon yadda za a kare."

- Ayo Fayose

Rikicin PDP: An caccaki matsayar Ayo Fayose

Masu bibiyar al’amura da kuma wasu ‘ya ‘yan PDP sun soki Fayose, sun tuna masa irin gatar da jam’iyyar ta yi masa a baya.

Wani mai suna Soultie1988 a X ya maida masa martani cewa yanzu an daina yayin sa a siyasa, tauraruwarsa ta dushe a Ekiti.

Kara karanta wannan

Yar’adua, Saraki da sauran gidajen siyasa 10 da suka fi shahara a Najeriya

Olorogun Ernest ya rubuta:

"Ban taba tunanin abubuwa za su lalace haka a PDP ba. Ba za ta yiwu ka tsaya ka na kallo ba alhali ka na cikin masu ruwa da tsaki."
"Meyasa ka ke yi wa jam’iyyar nan da ta ba ka kusan koma a rayuwa? A wani dalili?"

- @Esteembehemoth

Nwoba Kelechi Nelson ya ce Fayose ya ji kunya, ya bari APC ta na wulakanta jam’iyyar da ta sa ya zama gwamnan jiharsa.

PDP ta dakatar da Fayose da wasu 'ya 'yanta

A zaben 2023, Ayo Fayose ya na cikin wadanda ake ganin sun juyawa jam’iyyar PDP baya, su ka goyi bayan wasu ‘yan takaran APC.

Da aka tashi hukunta wadanda ake zargin sun yi zagon-kasa a zaben na 2023, har da Fayose da wasu na kusa da shi abin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng