Kanin Tsohon Gwamna Ya Ayyana Kansa Shugaban PDP, Ya Kori Atiku, Wike da Sauransu

Kanin Tsohon Gwamna Ya Ayyana Kansa Shugaban PDP, Ya Kori Atiku, Wike da Sauransu

  • Rigimar jam'iyyar PDP ta sauya salo bayan kanin tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya ayyana kansa shugabanta
  • Kanin tsohon gwamnan Ekiti mai suna Isaac Fayose ya ce daga yau shi ne shugabanta duk wanda ba yarda ba ya je kotu
  • Hakan ya biyo bayan rikicin da ya barke a PDP da ke neman raba ta gida biyu bayan tsaginta ya dakatar da shugabanta, Umar Damagum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ekiti - Yayin da ake rikicin jam'iyyar PDP, kanin tsohon gwamna ya ayyana kansa a matsayin sugabanta.

Kanin tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya ce ya karbi ragamar shugabancin jam'iyyar saboda rigimar da ake yi.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya shiga matsala da ɗan Majalisa ya maka shi a kotu da hadimansa 2

Dan uwan tsohon gwamnan ya kori Atiku da Wike a PDP bayan ayyana kansa shugabanta
Kanin tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ya ayyana kansa shugaban PDP inda ya kori Atiku da Wike. Hoto: @siccof.
Asali: Twitter

Kanin Fayose ya bayyana kansa shugaban PDP

Isaac Fayose ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da @OgbeniDipo ya wallafa a shafin X a daren jiya Juma'a 12 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isaac bayan tabbatar da kansa a matsayin shugabanta, ya sallami yayansa, Ayodele Fayose da sauran jiga-jiganta.

Ya ce duk wanda bai yarda da abin da ya aikata ba ka da ya je sakatariyar ta da rigima, su hadu a kotu kawai.

Har ila yau, ya kori dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar da Ministan Abuja, Nyesom Wike daga jam'iyyar.

Fayose ya kori Damagum da gwamnan PDP

Bayan sallamar jiga-jigai, Fayose ya kuma kori shugabanta, Umar Damagum da gwamnan Oyo, Seyi Makinde.

A cikin faifan bidiyon ya bukaci jami'an tsaron da ke sakatariyar jam'iyyar na Wadata Plaza da su mika masa makullan ofishin.

Kara karanta wannan

Atiku ya amince gwamnan Bauchi ya zama dan takarar shugaban kasa na PDP a 2027?

Fayose musamman ya kira sunan Atiku inda ya ce ya zama matsala ga PDP tare da zarginsu da yiwa jam'iyyar zagon-kasa.

Kotu ta hana dakatar da Damagum

Kun ji cewa yayin da rikicin PDP ke kara ƙamari, kotu ta shiga lamarin inda ta dakatar da matakin kwamitin zartarwa.

Babbar Kotun Tarayya da ke birnin Abuja ta haramta dakatar da Damagum daga mukaminsa na shugaban PDP.

Wannan na zuwa ne bayan tsagin jam'iyyar PDP ta dakatar Umar Damagum a jiya Juma'a 11 ga watan Oktoban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.