Tsadar Rayuwa: Shugaban PDP Ya Bayyana Masu Shan Wuya a Gwamnatin Tinubu
- Muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagum ya yi magana kan halin ƙuncin da ƴan Najeriya suke ciki
- Shugaban na PDP ya bayyana cewa waɗanda suka siyar da ƙuri'unsu a lokacin zaɓen 2023 sun fi kowa shan wahala a yanzu
- Damagum ya ba da shawarar ya kamata a mayar da hankali wajen samar da shugabanni nagari domin damƙa musu ragamar jagoranci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya yi magana kan halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan.
Umar Damagum ya bayyana cewa ƴan Najeriyan da suka karɓi wani abu suka yi zaɓe a 2023 su ne suka fi shan wahala a yanzu.
Jaridar Daily Trust ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake magana bayan wata ganawar sirri da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a ranar Juma’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban jam'iyyar PDP ya yi shaguɓe
Damagum ya yi shaguɓe ga ƴan Najeriya da ke goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, inda ya ce yanzu haka suna shan wahala saboda siyar da ƙuri'unsu da abubuwa irinsu taliya da atamfofi, rahoton Sahara Reporters ya tabbatar.
"Jam’iyyar APC ba ta taɓa shirin yin mulki ba, to wane abin arziƙi ne za a iya samu daga gare su?"
"Waɗanda suka karɓi taliya da atamfa domin kawo wannan gwamnati sun fi kowa shan wahala, kuma wannan ya isa ya zama darasi."
"Dole ne mu nemi shugabanni masu nagarta waɗanda a shirye suke su yi jagoranci da gaske, ba wai kawai masu cewa ‘Emilokan’ ba."
- Umar Iliya Damagum
Hakan na zuwa ne bayan wani ɓangare na kwamitin gudanarwa na PDP na ƙasa (NWC) ya dakatar da Damagum da sakataren jam'iyyar na ƙasa, Samuel Anyanwu.
Kotu ta hana dakatar da Damagum
A wani labarin kuma, kun ji kotun tarayya ta yi hukunci bayan wani tsagin PDP ya dakatar da shugaban jam'iyyar Umar Damagum daga muƙaminsa.
Kotun a ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Peter Lifu ta haramtawa kwamitin zartarwa (NEC) da majalisar amintattu (BOT) dakatar da Damagum.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng