Damagum: Guguwar Adawa na Shirin Kifar da Shugaban PDP, Ana Shirya Makarkashiya

Damagum: Guguwar Adawa na Shirin Kifar da Shugaban PDP, Ana Shirya Makarkashiya

  • Barakar PDP na kara kamari yayin da wasu daga cikin yan jam'iyyar ke kalubalantar shugabancin Ambasada Umar Damagum
  • A ranar 24 Oktoba za a gudanar da taron kwamitin zartarwa na PDP, kuma wasu yan jam'iyyar na shirin maye gurbin shugaba na kasa
  • Daga cikin masu neman kujerar Ambasada Damagum akwai Injiniya Conrad Utaan, ya kuma ce ana bukatar sauya shugabancin PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, AbujaYayin da PDP ke shirin gudanar da babban taronta na Kwamitin Zartarwa a ranar 24 Oktoba, 2024, wasu na son a tsige shugaban jam'iyyar.

Masu adawa da jagorancin shugaban PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum na kara daura damara wajen tube shi daga mukaminsa.

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gida: Jam'iyyar APC ta dare gida 2, gwamna ya ja zugarsa

Damagum
Ana kokarin cire shugaban PDP daga mukaminsa Hoto: Auwal Musa Muhammad Kaska
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa wasu bayanai sun nuna yadda masu ‘yan PDP daga Arewa ta Tsakiya su ka tattauna kan maye gurbin Ambasada Damagum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu baraka a jam'iyyar PDP

Jaridar The Nation ta tattaro cewa wasu ‘yan PDP sun gana domin lalubo wanda zai maye gurbin Ambasada Umar Damagum a matsayin shugaban jam’iyyar.

PDP ta fada rikici tun bayan zaben fitar da dan takara na shugaban kasar PDP, inda aka yi nasarar tsayar da Atiku Abubakar a matsayin dan takarar jam’iyyar.

An samu masu son shugabancin PDP

A tattaunawarsu da manema labarai a Abuja, daya daga cikin masu neman kujerar Ambasada Damagum, Injiniya Conrad Utaan ya ce PDP na bukatar sauyi.

Injiniya Utaan, ya fito daga yankin Arewa ta Tsakiya kamar tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Dr Iyorchia Ayu.

Kara karanta wannan

Atiku ko Wike? Shugabanni sun bayyana wanda ya haddasa rikicin da ya mamaye PDP

An rasa gano wanda ya haddasa rikicin PDP

A baya kun ji cewa jagororin jam'iyyar PDP sun gaza cimma matsaya kan wanda su ke zargi da kokarin kawo baraka a cikin jam'iyyarsu tun bayan zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa.

A taron jam'iyyar da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja, wasu daga cikin yan PDP sun zargi Ministan Abuja, Nyesom Wike da haddasa rikicin, wasu kuma sun zargi Alhaji Atiku Abubakar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.