Rikicin Cikin Gida: Jam'iyyar APC Ta Dare Gida 2, Gwamna Ya Ja Zugarsa

Rikicin Cikin Gida: Jam'iyyar APC Ta Dare Gida 2, Gwamna Ya Ja Zugarsa

  • Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu zai iya fuskantar matsala bayan wasu daga cikin yan jam'iyyarsa ta APC sun daina goyon bayansa
  • APC ta rabu, yayin da wasu daga cikin yan APC su ka ware kansu karkashin jagorancin Ibrahim Lamido domin kalubalantar gwamnan
  • Tsagin Lamido ya bayyana cewa ba zai fita daga cikin APC ba, amma za su ware gefe guda domin ba su gamsu da yadda gwamnan ke mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto - Rikicin cikin gida ya kunno kai cikin jam’iyyar APC a jihar Sokoto yayin da aka samu masu adawa da salon mulkin gwamna Ahmed Aliyu.

Kara karanta wannan

Boko haram: Sanata Ndume ya fadi gaskiya kan kai masa hari

Rahotanni sun bayyana cewa sabon tsagin ya bullo a jam’iyyar na karkashin jagorancin Ibrahim Lamido, sai kuma masu goyon bayan gwamnan da Sanata Aliyu Magatakarda ke jagoranta.

Sokoto
APC ta rabu a Sakkwato Hoto: Ahmad Aliyu Sokoto
Asali: Facebook

Jaridar BBC Hausa ta tattaro cewa wadanda ba sa goyon bayan gwamna Ahmed Aliyu sun dauki kwararan matakai da ke nuna cewa ba sa tare da tafiyar gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu marasa goyon bayan gwamnan Sakkwato a APC

Wasu daga cikin yan jam’iyyar APC da ke tsagin Ibrahim Lamido sun jaddada rashin goyon baya ga gwamna Ahmed Aliyu, inda su ka dauki matakai.

Wasu daga cikinsu sun yi murabus daga mukaman da su ke rike da shi wanda gwamnatin jihar Sakkwato ta nada su saboda an samu sabanin tafiyar siyasa.

Sakkwato: Dalilin rashin goyon bayan gwamna

Daya daga cikin kusoshi a tsagin Ibrahim Lamido na APC a Sakkwato, Hon Yakubu Sani ya bayyana cewa sun bi sabuwar tafiyar saboda akwai alamun gudanar da shugabanci na gari.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi dalilin kawo manufofin tattalin da suka jawo wahalar rayuwa

Ya jaddada cewa ba za su sauya jam’iyya ba, amma za su samar da tafiyarsu da za ta kalubalanci rashin gaskiya a mulkin jihar.

Gwamnatin APC ta warewa masallatai N95.4m

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin APC da ke mulki a jihar Sakkwato ta bayyana ware makudan kudi domin gyaran wasu masallatan Juma’a.

Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana cewa gwamntinsa ta amince da kashe Naira miliyan 95.4 domin gyara masallatan Juma’a 87 a fadin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.