An Gano Yadda Aka ba APC Nasara bayan Yarjejeniya da Gwamnan PDP Ya Yi da Akpabio
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi yarjejeniya tsakanin PDP da APC domin sadaukar da karamar hukuma daya a jihar Akwa Ibom
- Uban gidan Godswill Akpabio a siyasa, Michael Afangideh ya tabbatar da cewa PDP ce ta lashe zaben karamar hukumar Essien Udim
- Afangideh ya ce Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno ya sadaukar da karamar hukumar ga Akpabio saboda zaben 2027 da ake tunkara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Akwa Ibom- Bayanai sun fara fitowa kan yadda APC ta yi nasara a karamar hukuma daya jihar Akwa Ibom a zaben kananan hukumomi.
Wani jigo kuma uban gidan Godswill Akpabio a siyasa ya ce PDP ce ta ci zabe a karamar hukumar Essien Udim a jihar.
Yarjejeniya tsakanin Gwamnan da Akpabio
Dan siyasar mai suna Michael Afangideh ya fadawa Premium Times cewa yarjejeniya aka yi da Gwamna Umo Eno da Godswill Akpabio.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Afangideh ya ce Gwamna Umo Eno ya yi yarjejeniyar domin ba Akpabio karamar hukumarsa saboda siyasa a zaben 2027.
Ya ce an yi kulla yarjejeniyar ce tsakanin Sanata Akpabio da Gwamna Eno da kuma shugabannin PDP saboda maslahar siyasarsu ta 2027.
Yadda APC ta samu nasara a zaben kananan hukumomi
Hakan ya biyo bayan sanar da APC a matsayin wacce ta yi nasara a zaben kananan hukumomi da hukumar zaben jihar (AKISIEC) ta yi.
Jam'iyyar PDP ta lashe dukan kananan hukumomi 30 da ke jihar a zaben da aka gudanar a karshen makon da ya gabata.
An gudanar da zaben ne a cikin fargaba bayan yan daba sun bankawa ofishin hukumar zaben jihar (AKISIEC) wuta ana shirin gudanar da zaben kananan hukumomi.
APC ta yi nasara a zaben Akwa Ibom
Kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi nasara yayin da aka sanar da sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Akwa Ibom.
Jam'iyyar ta samu nasarar lashe kujeru 30 cikin 31 na ƙananan hukumomin jihar da aka yi a ranar Asabar 5 ga watan Oktoban 2024.
Hukumar zaben jihar, AKISIEC ita ta sanar da sakamakon zaben da aka gudanar a fadin jihar a ranar Lahadi 6 ga watan Oktoban 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng