Jagora a APC Ya Sake Taso Ganduje a Gaba, Ya Yi Masa Barazana a Jam'iyya

Jagora a APC Ya Sake Taso Ganduje a Gaba, Ya Yi Masa Barazana a Jam'iyya

  • Wani jagora a APC ya ba Abdullahi Umar Ganduje wa'adin kwanaki bakwai kan ya yi murabus daga shugabancin NWC
  • Alhaji Saleh Zazzaga ya aike da sabuwar wasiƙa ga shugaban na jam'iyyar APC inda ya nemi ya sauka daga muƙaminsa
  • Zazzaga wanda bai yi nasara ba a kotu kan yunƙurin tsige Ganduje, ya ce zai koma kotu idan wa'adin ya cika bai sauka ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Jagora a jam’iyyar APC, Alhaji Saleh Zazzaga, ya ba shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, wa'adin kwanaki bakwai ya sauka daga kan muƙaminsa.

Wannan sabon yunƙurin na Alhaji Saleh Zazzaga na zuwa ne biyo bayan rashin nasarar da ya yi a kotu kan ƙarar neman a tsige Abdullahi Ganduje.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan PDP ya fadi hanyar da za a ceto Najeriya

An bukaci Ganduje ya yi murabus
An ba Ganduje wa'adin kwana bakwai kan ya yi murabus Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Wane wa'adi aka ba Ganduje a APC?

Jagoran na APC ya ba Ganduje wa'adin ne a cikin a wata sabuwar wasiƙa da ya aike masa da ita, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Post ta ce da yake jawabi ga manema labarai jiya a Jos, AlhajI Saleh ya bayyana cewa an aika da kwafin wasikar ga shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Wasikar ta je wajen Godswill Akpabio, Tajudeen Abbas, da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC).

Jagoran na APC ya jaddada cewa wa’adin kwanaki bakwai wanda ya fara daga ranar Litinin zai ƙare ne a mako mai zuwa, kuma rashin yin murabus ɗin na Ganduje zai zai sa ya ƙara ɗaukar matakin shari’a.

Ana so Ganduje ya rabu da shugabancin APC

A cewarsa sun yi amfani da hanyoyi daban-daban na cikin gida kan rikicin, amma Ganduje ya tsaya tsayin daka wajen ƙin rabuwa da kujerar da bisa kundin tsarin mulkin jam’iyyar ta yankin Arewa ta Tsakiya ce.

Kara karanta wannan

Ana cikin tsadar rayuwa Tinubu ya fadi lokacin da 'yan Najeriya za su gode masa

Alhaji Saleh Zazzaga ya kuma ƙara da cewa Ganduje yana fuskantar shari’a kan zargin cin hanci da rashawa a jihar Kano, lamarin da a cewarsa yana ƙara zubar da mutuncin jam’iyyar.

Ya yi kira ga Ganduje da ya gaggauta yin murabus domin dawo da dimokuradiyyar cikin gida da kuma mutunta yarjejeniyoyin tsarin karɓa-karɓa na jam’iyyar. 

Ɗaruruwa ƴan NNPP sun koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya sake gigita NNPP mai mulki a jihar Kano yayin da ya karbi 'yan Kwankwasiyya.

Sanata Barau Jibrin ya karɓi ɗaruruwan ƴan jam’iyyar NNPP a fadin kananan hukumomin 44 na jihar Kano zuwa APC mai adawa a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng