Ba a Warware Batun Ganduje ba, Kotu Ta Yi Hukunci kan Kujerar Shugaban Jam'iyyar LP

Ba a Warware Batun Ganduje ba, Kotu Ta Yi Hukunci kan Kujerar Shugaban Jam'iyyar LP

  • Babbar kotun tarayya da ake zamanta a birnin Abuja ta yi hukunci kan taƙaddamar shugabanci da ta dabaibaye jam'iyyar Labour Party (LP)
  • Alƙalin kotun ya tabbatar da Barista Julius Abure a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙasa a hukuncin da ya yi a ranar Talata, 8 ga watan Oktoban 2024
  • Mai shari'a Emeka Nwite ya umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta amince da Abure a matsayin halastaccen shugaban LP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tabbatar da Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar Labour Party (LP) na ƙasa.

Kotun tarayyar ta zartar da hukuncin ne a ranar Talata, 8 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

Bam ya fashe a sakatariyar jam'iyyar APC, an samu bayanai

Kotu ta yi amince da shugabancin Julius Abure a LP
Kotu ta tabbatar da shugabancin Julius Abure a LP Hoto: @NgLabour
Asali: Twitter

Wane hukunci kotu ta yanke?

Alƙalin kotun mai shari'a Emeka Nwite, ya tabbatar da shugabancin Abure da sahihancin babban taron jam'iyyar da aka yi a Nnewi a watan Maris 2024, cewar rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari'a Emeka Nwite ya umarci hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) da ta amince da Abure a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da zancen.

Jam'iyyar Labour Party dai ta shigar da hukumar INEC ƙara a gaban kotun a shari'ar mai lamba FHC/ABJ/CS/1271/2024.

"Na yi hukunci cewa bisa ga sahihan takardun da aka kawo, ƙoƙarin wanda ake ƙara na ƙin amincewa da shugabancin wanda ya shigar da ƙara bai yi nasara ba."
"Mai shigar da ƙara ya kawo hujjojinsa. Saboda haka ina umartar wanda ake ƙara ya amince da shugabancin jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Julius Abure, tare da ba ta duk wani haƙƙi da ƴancin da jam'iyyun da suka yi rajista a Najeriya suke da shi."

Kara karanta wannan

PDP ta birkice, an dakatar da mataimakin shugaban jam'iyya na ƙasa

- Mai shari'a Emeka Nwite

Karanta wasu labaran kan jam'iyyar LP

LP ta naɗa mace a muƙamin shugaba

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohuwar ministar kudi, Sanata Nenadi Usman, ta zama shugabar kwamitin riko na jam’iyyar Labour Party (LP) ta ƙasa.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka naɗa a kwamitin rikon kwarya domin aiki da Nenedi Usman shi ne Hon. Darlington Nwokocha, ɗan takarar sanatan Abia a 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng