Gwamnan APC Ya Fadi Babban Burin da Ya Ke Son Cimmawa a Zaben 2027

Gwamnan APC Ya Fadi Babban Burin da Ya Ke Son Cimmawa a Zaben 2027

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya shawarci jiga-jigan APC domin hada kai wurin samun nasara a zabe mai zuwa
  • Mai girma Abdullahi Sule ya ce ba shi da wani buri a duniya illa a zaben 2027 ya mika mulki ga gwamnatin jam'iyyar APC
  • Gwamnan ya ce mutane da dama ba za su gane bambancin ba har sai lokacin da ya bar ofis za su yi nadama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nassarawa ya yi magana kan zaben 2027 da ake tunkara.

Gwamna Abdullahi Sule ya ce babban burinsa shi ne mika mulki ga gwamnatin APC bayan kammala wa'adinsa.

Kara karanta wannan

'Zancen bur inji tusa', APC ta fadi abin da zai faru a hadakar Kwankwaso da Peter Obi

Gwamna ya bayyana shirinsa na miƙa mulki ga gwamnatin APC
Gwamna Abdullahi Sule ya ce burinsa shi ne mika mulki ga gwamnatin APC. Hoto: Abdullahi Sule.
Asali: Twitter

Gwamna ya fadi burinsa a zaben 2027

Gwamnan ya bayyana haka ne a jiya Litinin 7 ga watan Oktoban 2024 yayin ganawa da masu ruwa tsakin APC, da shafin Gov. Sule Abdullahi Mandate ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Sule ya ce mutane ba za su taba ganin illar rashinsu a ofis ba har sai sun bar wurin.

Ya ce ayyukan more rayuwa da dama da suka fara ba za su inganta ba har sai an mika mulki ga jam'iyyar APC a 2027, cewar Daily Nigerian.

"Kamar yadda ku ka sani da kuma wadanda ba su sani ba, babban buri na shi ne mika mulki ga gwamnatin APC a 2027."
"Abu mafi muhimmanci da ya kamata ku sani shi ne za ku ga bambanci ne bayan mun bar ofishin gwamna."
"Mutane da yawa suna zuwa nan cikin sauki su ganni su tafi, idan ba APC ce ta karbi mulki ba ko wanene kai ba zaka samu haka ba."

Kara karanta wannan

'Ba za mu ba Tinubu takara ba,' Jigon APC ya tono wani shiri kan zaben 2027

- Abdullahi Sule

Gwamna Sule ya ba jiga-jigan APC shawara

Gwamna Sule ya shawarci masu ruwa da tsakin APC da su hada kai wurin ba jam'iyyar nasara a zaben kananan hukumomi.

Har ila yau, gwamnan ya ce ya yafewa dukan wadanda suka yi masa laifi ko saba masa a zaben 2023 da ya wuce.

Za a yi zaben kananan hukumomi a Nasarawa

Kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Nasarawa ta ce ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi 13.

Shugaban NASIEC, Ayuba Wandai-Usman, ya ce za a gudanar da zaben ciyamomi da na kansilolin a ranar Asabar, 2 ga Nuwamba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.