"Durkusawa Wada:" Gwamnan Ribas Ya Fadi Dalilin ba Wike Hakuri
- Siminalayi Fubara ya bayyana cewa sai da ya yi kokarin ganin an kaucewa tashin hankali a jiharsa ta hanyar tattaunawa da Nyesom Wike
- Gwamnan ya ce ya roki tsohon Mai gidansa, Nyesom Wike da ya zubar da makamansa domin samun wanzuwar zaman lafiya a jihar
- Amma a cewar Fubara, Wike bai karbi rokon da ya yi masa ba, yanzu haka ana fama da rikicin da ake zargin da sa hannun magoya bayan Wike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Rivers - Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya roki Ministan Abuja kuma tsohon uban gidansa, Nyesom Wike kan samuwar zaman lafiya a jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa sai da ya durkusa har kasa domin lallaba Nyesom Wike, wanda tsohon gwamnan Ribas ne kan dakatar da tashin hankali a jihar.
A hira da ya yi da tashar Channels, Siminalayi Fubara ya bayyana dalilinsa na ba Nyesom Wike hakuri har ta kai ga durkusawa har kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike: Gwamnan Ribas ya nemi sulhu
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa gwamnan jihar Ribas, Siminalyi Fubara ya bayyana cewa sai da ya yi kokarin a samu fahimtar juna tsakaninsa da Wike.
Gwamna Fubara ya ce ya yi haka ne domin a samu zaman lafiya mai dorewa a jihar, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.
Gwamna Fubara ya gamsu da zaben Ribas
Gwamna Siminalayi Fubara ya bayyana gamsuwa kan yadda ya dage wajen tabbatar da gudanar da zabe a jiharsa duk da bijirewar magoya bayan Wike da yan jam'iyyarsa.
Ya bayyana cewa yanzu magana ake yi ta ci gaban al'umar jihar Ribas ba wasu tsirarun mutane ba, inda ya kara da cewa akwai bukatar kowa ya zubar da makamansa.
Tinubu ya yi gargadi kan rikicin Ribas
A baya mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gargadi masu tayar da hankula bayan gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Ribas, ya nemi a dawo da doka da oda.
Gargadin shugaban na zuwa bayan an samu tashe tashen hankula da kone-kone da ya biyo bayan zaben kananan hukumomi da ya gudana a ranar Asabar duk da umarnin kotu na hana zaben.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng