Tinubu Ya yi Magana kan Kone Kone a Rivers, Ya ba Yan Sanda Zazzafan Umarni

Tinubu Ya yi Magana kan Kone Kone a Rivers, Ya ba Yan Sanda Zazzafan Umarni

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi gargadi bayan rikici ya biyo bayan zaben kananan hukumomi a jihar Rivers
  • Bola Tinubu ya ba sufeton yan sandan Najeriya umarnin shawo kan rikicin tare da tabbatar da doka da oda a dukkan sassan jihar
  • Shugaban kasar ya bayyana irin rawar da kotu za ta taka wajen warware dukkannin matsaloli da aka fuskanta a Ribas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana bayan rikicin bayan zabe ya fara ƙamari a jihar Rivers.

Yan daba sun fara kone kone a ƙanana hukumomin jihar Rivers domin nuna adawa da zaben da aka yi a a makon jiya.

Kara karanta wannan

Abubuwa 3 da suka jawo karamar jami'yya ta buga APC da PDP a kasa a Rivers

Shugaba Tinubu
Tinubu ya yi gargadi kan rikicin Rivers. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Hadimin shugaban kasa a harkokin sadarwa, Bayo Onanuga ne ya wallafa bayanin Bola Tinubu a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya yi kira ga gwamnan Rivers

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci gwamna Siminalayi Fubara da dukkan yan siyasa a Rivers su mayar da wuƙaƙensu.

Shugaban kasar ya ce ya zama dole a girmama doka da oda tare da yin taka-tsantsan kan rikicin da yake faruwa jihar.

Rivers: Tinubu ya ba yan sanda umarni

Bola Ahmed Tinubu ya umarci yan sandan Najeriya su tabbatar da tashin hankali bai cigaba ba jihar Rivers.

Shugaban kasar ya ce ya zama dole jami'an tsaro su tabbatar da sun kare rayukan da dukiyoyin al'umma yayin tabbatar da tsaro a jihar.

Ya ce ba yadda za a yi a zuba ido wasu bata gari suna lalata kayayyakin gwamnati da aka samar da kudin al'umma.

Kara karanta wannan

Neman Tazarce a 2027: Manyan 'yan siyasar Kano da ke goyon bayan Shugaba Tinubu

Shugaba Tinubu ya yi kira kan tafiya kotu

Shugaban kasar ya bukaci dukkan wadanda ba su ji dadin yadda zaben ya gudana ba su mika korafi a kotu.

Ya ce kotu na shirye domin warware duk wani rikici da ya shafi siyasa kuma jihar Rivers ba za ta kaucewa hakan ba.

An fara yunkurin hana Tinubu takara a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa kusa a APC kuma mai fashin baki, Garus Gololo ya ce za su tabbatar da cewa Bola Tinubu bai samu takara ba a 2027.

Dakta Garus Gololo ya bayyana cewa akwai abubuwa da dama da gwamnatin tarayya ta ke yi wanda suka jefa al'umma a wahala.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng