Yan Daba Sun Cinna Wuta a Ƙananan Hukumomin Rivers, Sun Yi Fashe Fashe

Yan Daba Sun Cinna Wuta a Ƙananan Hukumomin Rivers, Sun Yi Fashe Fashe

  • Rikicin bayan zabe ya kunno kai a jihar Rivers bayan kammala takarar kananan hukumomi da ya gudana a ranar Asabar da ta wuce
  • An ruwaito cewa yan daba sun fara cimma wuta a sakatariyar kananan hukumomi domin nuna adawa da zaben da ya gudana
  • Hakan na zuwa ne bayan rundunar yan sanda ta janye jami'anta a dukkan sakatariyar kananan hukumomin jihar bayan zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Rikici na cigaba da ɗaukan sabon salo bayan zaben kananan hukumomi da aka yi a Rivers.

An ruwaito cewa wasu yan daba dauke da makamai sun fara kone kone a wasu daga cikin sakatariyar kananan hukumomin jihar.

Kara karanta wannan

Rikici ya barke a Ribas, 'yan bindiga sun farmaki sabon shugaban karamar hukuma

Fubara
Ana rikicin bayan zabe a Rivers. Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa a yanzu haka yan dabar sun kona sakatariyar ƙananan hukumomin jihar guda biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kona sakatariyar karamar hukuma a Rivers

Rahotanni da suke fitowa sun nuna cewa yan daba dauke da makamai na kai hare hare a hedikwatar kananan hukumomin jihar.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa yan daba sun kona sakatariyar kananan hukumomi biyu a jihar a yau Litinin.

Wace sakatariyar aka kona a Rivers?

Da misalin karfe 11:00 na safiyar yau ne yan daba suka cinna wuta a sakatariyar karamar hukumar Eleme ta jihar Rivers.

Haka zalika an ruwaito cewa yan daba sun kona sakatariyar da ofishin ciyaman na karamar hukumar Ikwerre saboda kin yarda da zaben kananan hukumomi.

An yi fashe fashe a karamar hukumar Emohua

A wani rahoton kuma an tayar da abubuwan fashewa a karamar hukumar Emohua da suka girgiza gine gine kuma suka jawo barna mai dimbin yawa.

Kara karanta wannan

Ribas: Mummunar gobara ta babbake sakatariyar karamar hukuma, bayanai sun fito

Lamarin ya faru ne yayin da shugaban karamar hukumar, David Omereji yake kokarin rantsar da mataimakinsa da kansiloli.

PDP ta yabi Fubara kan zaben jihar Ribas

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Sanata Bala Mohammed ya yaba da yadda aka gudanar da zabe a jihar Ribas.

A ranar Asabar ne gwamnatin Simi Fubara ta bijirewa umarnin kotu da barazanar jami'an tsaro aka yi zaben kananan hukumomi a jihar Rivers.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng