Gwamna Ya Rasa Karamar Hukuma a Hannun Bakuwar Jam'iyya, APC Ta Karbi Kujera 1

Gwamna Ya Rasa Karamar Hukuma a Hannun Bakuwar Jam'iyya, APC Ta Karbi Kujera 1

  • Yayin da aka sanar da sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Rivers, jam'iyyar AA ta samu nasarar lashe kujera daya
  • Hukumar zaben jihar ta RSIEC ta tabbatar da nasarar jam'iyyar AA ne a yau Lahadi 6 ga watan Oktoban 2024
  • A jiya Asabar da aka gudanar da zaben, jam'iyyar APP ta yi nasarar lashe kujerun kananan hukumomi 22 cikin 23

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Rivers - Hukumar zaben jihar Rivers (RSIEC) ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi.

Hukumar RSIEC ta sanar da sakamakon zaben karamar hukumar Etche ne a yau Lahadi 6 ga watan Oktoban 2024.

Gwamna ya yi rashin nasara a karamar hukuma bayan sanar da sakamakon zabe
Jam'iyyar AA ta samu nasara a zaben kananan hukumomi a Rivers. Hoto: @emmaikumeh/splendornino.
Asali: Twitter

Rivers: Jam'iyyar AA ta yi nasara a zabe

Shugaban hukumar, Adolphus Enebeli ya ce Uzodinma Nwafor na jam'iyyar AA shi ya yi nasara a zaben, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Benue: Jam'iyyar APC ta ba da mamaki a zaben kananan hukumomi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Enebeli ya ce Nwafor ne kaɗai ya yi nasara a jam'iyyar AA inda ya ce APP ce ta lashe sauran kujerun.

Hakan ya biyo bayan sanar da sakamakon zaben kananan hukumomi 22 cikin 23 da APP ta yi nasara a jiya Asabar.

Jam'iyyar APP har ila yau, ita ta lashe kujerun kansiloli 19 da ke karamar hukumar Etche a jihar.

Yadda APP ta cinye kujeru a Rivers

A gaba daya kujerun kansiloli fiye da 300 da aka gudanar, APP ta yi nasarar tashi da guda 314.

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ya samu kujerar kansila daya sai kuma LP da kujera daya sannan SDP ma guda daya.

Har ila yau, jam'iyyar YPP ta yi nasarar tashi da kujera daya ita a zaɓen da aka yi a jiya Asabar 5 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

Fubara ya lallasa Wike: Bakuwar jam'iyya ta lashe kujerun ciyamomi 22 a Ribas

Rivers: APP ta lashe zaben kananan hukumomi

Kun ji cewa jam’iyyar APP ta cinye kusan komai da aka gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi a jihar Ribas.

Shugaban hukumar RSIEC, Adolphus Enebeli, ya ce APP ta yi nasara a kananan hukumomi 22 cikin 23 da ke Ribas.

Kotu ta kawowa zaben cikas amma wannan bai hana gwamna Simi Fubara ya goyi bayan a shirya zabe a Ribas ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.