Benue: Jam'iyyar APC Ta Ba da Mamaki a Zaben Kananan Hukumomi

Benue: Jam'iyyar APC Ta Ba da Mamaki a Zaben Kananan Hukumomi

  • Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Benue ta samu gagarumar nasara a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar a ranar Asabar, 5 ga watan Oktoba
  • Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar, ya sanar da cewa APC ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi 23 da kansiloli 276
  • Richard Tombowua wanda ya sanar da sanar da sakamakon a ranar Lahadi, ya bayyana cewa zaɓen ya gudana cikin gaskiya da adalci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Jam’iyyar APC mai mulki ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi da kansiloli a zaɓen ƙananan hukumomin da aka yi a jihar Benue.

A jiya Asabar, 5 ga watan Oktoban 2024 aka gudanar da zaɓen na ƙananan hukumomi a jihar.

Kara karanta wannan

APC Ta ƙara kinkimo rigima a jihar Kano ana shirin zaɓen kananan hukumomi

APC ta lashe zabe a Benue
APC ta lashe kujerun ciyamomi da kansiloli a Benue Hoto: Fr. Hyacinth Iormem Alia
Asali: UGC

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Benue, Richard Tombowua, ya sanar da sakamakon zaɓen a ranar Lahadi, 6 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta lashe zaɓe a Benue

Richard Tombowua ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi 23 da na kansiloli 276 a zaɓen da aka gudanar, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

"Zaɓen da aka gudanar jiya a faɗin jiha ya gudana lami lafiya ba tare da tangarɗa ba. An gudanar da shi cikin gaskiya da adalci kuma jami’an zaɓe sun miƙa dukkanin sakamakon da aka samu daga rumfunan zaɓe."
"Daga sakamakon zaɓen, jam’iyyar APC ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi 23 da kansiloli 276."

- Richard Tombowua

Shugaban hukumar zaɓen ya bayyana cewa biyar daga cikin jam’iyyun siyasa takwas da suka gabatar da jerin sunayen ƴan takara ne suka shiga zaɓen na ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Rivers: Zanga zanga ta barke ana tsaka da gudanar da zabe, an gano dalili

Gwamnan Benue ya ba da hutu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Benue ƙarƙashin jagorancin Hyacinth Alia ta ayyana ranar Juma'a, 4 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu.

Gwamnatin ta ba da hutun ne gabanin zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a yi a ranar, Asabar 5 ga watan Oktoban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng