Gwamna Ya Yaki Jami'an Tsaro, APC da PDP, Ya Cinye Komai a Zaben Kananan Hukumomi

Gwamna Ya Yaki Jami'an Tsaro, APC da PDP, Ya Cinye Komai a Zaben Kananan Hukumomi

  • Jam’iyyar APP ta cinye kusan komai da aka gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi a jihar Ribas
  • Shugaban hukumar RSIEC, Adolphus Enebeli, ya ce APP ta yi nasara a kananan hukumomi 22 cikin 23 da ke Ribas
  • Kotu ta kawowa zaben cikas amma wannan bai hana gwamna Simi Fubara ya goyi bayan a shirya zabe a Ribas ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Rivers - Jam’iyyar APP ta lashe zabe a kananan hukumomi 22 daga cikin 23 da ake da su a jihar Ribas a ranar Asabar.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ribas, Adolphus Enebeli, ya sanar da sakamako bayan an yi zaben.

Ribas
Jam'iyyar APP ta lashe zaben kananan hukumomin jihar Ribas Hoto: @emmaikumeh/splendornino
Asali: Twitter

APP za ta karbe kananan hukumomin Ribas

Rahoton The Cable ya ce Alkali Adolphus Enebeli ya ba da sanarwar ne a yammacin ranar Asabar a garin Fatakwal.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ja daga, ya ce zai iya rasa ransa saboda adalci a zaben gobe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi, shugaban na RSIEC ya bayyana cewa jam’iyyar hamayya ta APP ta yi nasara a kananan hukumomi 22.

Duk da APP jam’iyyar adawa ce, an samu labari gwamna Simi Fubara ya umarci mabiyansa a Ribas su koma cikinta.

Ana rikici kan zaben jihar Ribas

Yayin da APC da PDP su ka nesanta kansu da zaben Ribas, magoya bayan gwamnan jihar Ribas a APP sun yi maraba da shi.

Zaben ya zo da matsaloli domin a farkon Satumba kotu ta hana hukumar RSIEC gudanar da zabe da rajistar shekarar 2023.

Bayan nan kuma aka ji wata kotun tarayya da ke Abuja ta haramtawa INEC ba hukumar RSIEC rajistar masu kada kuri’a.

Ana cikin wannan rikici ne dai gwamna Simi Fubara ya dage sai an gudanar da zaben, kuma aka yi ikirarin APP ta lashe.

Kara karanta wannan

An rikita Ribas, masu zanga zanga sun fusata, sun dunguma ofishin hukumar zabe

Sakamakon karamar hukuma 1 ya rage a Ribas

Sakamakon zaben karamar hukumar Etche ne kurum ba a sanar ba saboda ana kokarin kirga kuri’un da jama’a suka kada.

Rahoton tashar Channels ya ce nan gaba kadan ake sa ran za a san wanda zai zama shugaban karamar hukumar ta Etche.

Gwamnan Ribas a ofishin hukumar zabe

Rahotanni sun nuna yadda wasu matasa su ka fatattaki ƴan sanda daga ofishin hukumar zaɓen jihar Ribas a cikin makon nan.

Hakan na zuwa ne bayan rundunar ƴan sanda ta ce babu ruwanta da zaɓen kananan hukumomin Ribas saboda wani hukuncin kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng