AKISIEC: 'Yan Daba Sun Tafka Ta'asa, Sun Bankawa Ofishin Hukumar Zaɓe Wuta
- Wasu miyagu sun banka wuta a ofishin hukumar zaɓe AKISIEC da ke garin Ibiatuk a ƙaramar hukumar Ibiono a jihar Akwa Ibom
- Lamarin ya faru ne awanni kaɗan gabanin fara zaɓen kananan hukumomi yau Asabar, 5 ga watan Oktoba, 2025
- Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da kai harin amma ta ce bai hana zaɓe ba kuma miyagun ba su ci nasarar lalata kayayyakin zaɓe ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom - Sa'o'i kaɗan gabanin fara zaɓen kananan hukumomi a jihar Akwa Ibom, an bankawa ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta wuta.
Rahotanni sun nuna wasu miyagu da ake zaton ƴan daban siyasa ne sun ƙona ofishin hukumar zaɓe ta jiha watau AKISIEC da ke Ibiatuk a ƙaramar hukumar Ibiono Ibom.
Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan Akwa Ibom, ASP Timfon John ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, kamar yadda The Nation ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan sanda sun yi bayanin abin da ya faru
Ta ce babu wanda ya mutu sakamakon banka wutar kuma dukkan kayayyakin zaɓe na nan lafiya, babu abin da ya same su.
Timfon John ta ce duk da ƙona ofishin hukumar zaɓen, jama'a sun fito rumfunan zaɓensu domin kaɗa kuri'a a zaɓen ciyamomi da kansiloli da ke gudana yau Asabar.
A cewarta, rundunar ‘yan sandan ta tura karin jami’an tsaro zuwa ofisoshin AKISIEC da ke fadin jihar Akwa Ibom domin dakile duk wani yunkurin tada zaune tsaye.
Yadda zaɓe ke tafiya a Akwa Ibom
An tattaro cewa a yau Asabar, 5 ga watan Oktoba, 2024, ake gudanar da zaɓen kananan hukumomi a Akwa Ibom.
Bayanai sun nuna cewa babbar matsalar da aka fuskanta a zaɓen ita ce rashin isar kayayyaki da malaman zaɓe da wuri.
A rumfar zaɓe 001 da ke gunduma ta 14 a ƙaramar hukumar Uyo, har karfe 10:02 na safiya babu kayan zaɓe da malaman zaɓe, haka jami'an tsaro ma ba su je wurin ba.
Haka lamarin ya faru na rashin zuwan kayan zaɓen a Unit 2, Ward 11 a karamar hukumar Itu, kamar yadda Punch ta rahoto.
Zanga-zanga ta ɓarke a Rivers
A wani rahoton kuma magoya bayan ministan Abuja, Nyesom Wike sun fito kan tituna domin nuna adawarsu da zaɓen ƙananan hukumomin da ake yi a jihar Rivers.
Masu zanga-zangar sun buƙaci Gwamna Siminalayi Fubara da ya bi umarnin kotu wanda ya hana a gudanar da zaɓen a jihar
Asali: Legit.ng