Kwamacala: Gwamna Ya Nada 'Yarsa domin Maye Gurbin Matarsa a Ofishin 'First Lady'
- Kwanaki bayan mutuwar matarsa, Gwamna ya gabatar da 'yarsa domin maye gurbin ayyukan ofishin marigayiyar
- Gwamna Umo Eno ya tabbatar da nadin 'yarsa, Helen Eno domin zama a matsayin 'First Lady' na rikon kwarya
- Hakan na zuwa ne bayan mutuwar matarsa, Mrs Patience Umo Eno kimanin kwanaki tara kenan da suka gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno ya nada wacce za ta rike ofishin 'First Lady' bayan mutuwar matarsa.
Gwamna Eno ya tabbatar da nadin 'yarsa, Helen Eno domin rike ofishin marigayiyar, Patience Eno na rikon kwarya.
Gwamna ya nada 'yarsa a ofishin matarsa
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan ziyarar matar shugaban kasa, Remi Tinubu domin yi masa jaje, cewar rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Eno ya gabatar da 'yarsa, Helen inda ya ce za ta cigaba da ayyukan alheri da ofishin ya ke yi kafin mutuwar matarsa.
"Domin cigaba da ayyukan ofishin matar gwamna, ina gabatar muku da 'yata, Helen Eno saboda gudanar da ayyukan marigayiya."
"Helen za ta yi aiki kafada da kafada da mataimakin gwamna da kuma kwamishinar harkokin mata."
- Umo Eno
Eno ya bayyana kwarin guiwarsa kan kwarewar 'yar tasa inda ya ce yana da tabbacin za ta cigaba da ayyukan ofishin ba tare da matsala ba.
Matar Tinubu ta yaba da matakin gwamnan
A martaninta, Remi Tinubu da ta kai ziyara jihar domin jajantawa ta yaba da matakin da Gwamna Eno ya dauka.
Remi Tinubu ta ce hakan shi zai taimaka wurin cigaba da ayyukan da marigayiyar ta dauko domin mutunta ta.
Gwamna ya magantu bayan mutuwar matarsa
Kun ji cewa Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya yi magana kan rashin da ya yi na matarsa, Mrs Patience Eno.
Gwamnan ya fadi irin kewar matarsa da zai yi na tsawon rayuwarsa saboda irin gudunmawar da ta bayar a bangarori da dama.
Gwamnan ya yi godiya ga shugaba Bola Tinubu da yan jihar Akwa Ibom da sauran al'umma kan addu'o'in da suka yi mata.
Asali: Legit.ng