Shugaba Tinubu Ya Gama Tsara Sunayen Ministocin da Zai Kora daga Aiki, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu Ya Gama Tsara Sunayen Ministocin da Zai Kora daga Aiki, Bayanai Sun Fito

  • Bola Ahmed Tinubu ya gama tsara sunayen ministocin da zai ci gaba da aiki da su da waɗanda zai sallama daga aiki
  • Wasu rahotanni daga fadar shugaban ƙasa sun nuna tun ranar Alhamis aka yi tsammanin Tinubu zai saki sunayen amma ya canza shawara
  • Yanzu haka dai shugaban kasa yana birnin Landan na kasar Burtaniya inda ya tafi hutun shekara na tsawon mako biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Alamu masu karfi sun nuna shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya gama garambawul din da zai yi a majalisar zartaswar gwamnatinsa.

Wasu bayanai daga majiyoyi da dama a fadar shugaɓan ƙasa sun ce Tinubu ya gama tsara sunayen ministocin da zai kora da waɗanda za su ci gaba da aiki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da babban ɗan siyasa da wani shugaban al'umma a Najeriya

Shugaba Bola Tinubu
Shugaban ƙasa Bola Tinubu na dab da sakin sunayen ministocin da zai kora daga aiki Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Majiyoyin sun tabbatarwa jaridar Punch ranar Asabar cewa ana kyautata zaton shugaban ƙasar zai fitar da sunayen waɗanda ya kora ne bayan ya tafi hutu Landan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu dai ya tafi ƙasar Burtaniya, inda zai yi hutun mako biyu daga cikin hutunsa na shekara kamar yadda doka ta tanada.

Yadda aka matsawa Tinubu lamba

Tun bayan zanga-zangar da aka yi a watan Agusta, Tinubu ya fara fuskantar matsin lamba daga ciki da wajen APC kan ya kori ministocin da suka zama ƴan ɗumama kujera.

Duk da shugaban kasar ya sha gargaɗin ministocin kan gazawa, har yanzu babu wani sauyi a majalisar zartaswa in ban da ministar jin kai, Betta Edu da aka dakatar.

Yaushe Tinubu zai yi garambawul a gwamnatinsa?

Wasu jami'ai a fadar shugaban ƙasa da suka nemi a sakaya sunansu, sun ce da farko an yi tsammanin Tinubu zai saki sunayen ranar Alhamis da daddare amma ya canza shawara.

Kara karanta wannan

“An samu tsaro a Najeriya”: Ribadu ya fadi bambancin gwamnatin Tinubu da Buhari

A wata hira da Punch ranar Jumu'a, wata majiya ta ce:

"Tun jiya (Alhamis) muke sa ran sakin sunayen amma har yanzu shiru, ban san komai game da sunayen da ke ciki ba.
"Abin da na sani shi ne shugaban kasa ya faɗa mana yana son kara tunani kafin ya saki, wataƙila akwai sunayen da yake son canzawa."

Wata majiya ta daban, ita ma ta nemi a sakaya sunanta ta ce, “Na yi mamaki da sunayen ba su fito ba jiya (Alhamis), kusan an gama komai."

Haka zalika wani jami'i a fadar shugaban ƙasa ya musanta raɗe-raɗin cewa masu kafun ƙafa sun yi cincirindo a gidan shugaban kasa da ke ƙasar Burtaniya.

Ayodele ya buƙaci a kori ƙaramin minista

A wani rahoton kuma Primate Elijah Babatunde Ayodele ya yi kira da a gaggauta korar ƙaramin ministan man fetur, Heineken Lokpobiri.

Wannan kiran na Ayodele na zuwa ne a daidai lokacin da farashin man fetur ya tashi a Najeriya, wanda malamin ya yi hasashen cewa zai ƙara tashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262