Bola Tinubu Ya Ji Matsin Lamba, Ya Canza Lambar Yabon da Ya Ba Shugaban Majalisa
- A ƙarshe shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauya lambar girmamawar da ya ba kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas
- Shugaba Tinubu ya karɓi kuskuren da ya yi a farko, ya ɗaga ƙimar Abbas zuwa lambar yabo ta GCON maimakon CFR da ya sanar a baya
- Wannan na zuwa ne bayan ƴan majalisar wakilai sun yi fatali da CFR da Tinubu ya ba Abbas, suka nemi ya karrama shi da lamba mafi girma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya karɓi koken ƴan majalisar wakilan tarayya, ya sauya lambar yabon da ya ba Rt. Hon. Tajudeen Abbas.
Bola Tinubu ya karrama kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas da lambar girma ta GCON maimakon CFR da ya ba shi a baya.
Yadda majalisa wakilai ta fusata a farko
Idan ba ku manta ba a jawabinsa na ranar 1 ga watan Oktoba, Tinubu ya sanar da karrama kakakin majalisar wakilai da mataimakin shugaban majalisar dattawa da lambar yabon CFR.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai hakan ya haifar da zazzafar muhawara a zauren majalisar wakilai, inda suka yi fatali da CFR da aka ba Abbas kuma suka nemi a ba shi lambar yabo mafi girma.
Mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya ce Tinubu ya gamsu da matsayar ƴan majalisar kuma ya gyara kuskuren da ya yi.
Bola Tinubu ya ba Tajudeen Abbas GCON
A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X yau Juma'a, Bayo Onanuga ya ce Shugaban Ƙasa Tinubu ya ɗaga darajar Rt Hon. Tajudeen zuwa GCON maimakon CFR.
"Shugaba Tinubu ya gamsu da koken ƴan majalisar wakilai kuma ya amince da gyara kurkuren da ya yi.
"Sakamakon haka shugaban ƙasar ya ɗaga darajar kakakin majalisar wakilai, ya ba shi lambar girma ta GCON maimakon CFR kamar yadda doka ta tanada.
"Nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai da sauran jagororin majalisa da shugabar alƙalai da lambobin yabon da aka ba su a hukumance."
- Bayo Onanuga.
Tinubu na shirin sake fasalin haraji
Kuna da labarin a ranar Alhamis, kakakin majalisar wakilai, Abbas Tajudeen ya karanta wata wasika da shugaban kasa Bola Tinubu ya aiko masu
A cikin wasikar, Tinubu ya gabatarwa majalisar kudurori hudu da suka shafi sake fasalin haraji inda ya bukaci amincewarsu da gaggawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng