Rigima Ta Barke da Gwamna Ya Yi Fatali da Umarnin Mataimakinsa, Ya Fadi Matsayinsa
- Rigima tsakanin gwamna da mataimakinsa ta dauki sabon salo bayan fitar da sabuwar sanarwa a yau Juma'a
- Gwamna Godwin Obaseki na Edo ya caccaki mataimakinsa, Kwamred Philip Shaibu kan fitar da sanarwa a jihar
- Gwamnan ya ce Shaibu tsigagge ne kuma ba shi da wani mukami a gwamnati, ya yi fatali da umarnin da ya bayar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya kalubalanci mataimakinsa, Kwamred Philip Shaibu.
Obaseki ya caccaki Shaibu kan wata sabuwar sanarwa da ya fitar a yau Juma'a 4 ga watan Oktoban 2024.
Gwamnan Edo ya kalubalanci umarnin mataimakinsa
Gwamnan ya gargadi Shaibu ne a cikin wata sanarwa da Tribune ta samu ta bakin hadiminsa, Crusoe Osagie ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obaseki ya shawarci ma'aikatan jihar su yi watsi da sanarwar inda ya ce ba shi da wani mukami a gwamnatin Edo.
Gwamnan ya ce har yanzu Shaibu bai da ikon rike ofishin mataimakinsa gwamnan jihar saboda korarre ne.
Sanarwar gargadi da Shaibu ya fitar ga ma'aikata
Wannan na zuwa ne bayan mataimakin gwamnan, Philip Shaibu ya fitar da sanarwa inda ya ke gargadin ma'aikata a jihar.
Shaibu ya yi gargadin ne a shafinsa na Facebook a yau Juma'a 4 ga watan Oktoban 2024 kan dakile kwashe kayan gwamnati yayin da suke barin ofis.
Mataimakin gwamnan ya ce duk wanda ya bari aka yi barna kan kayayyakin gwamnati ko daga ofishinsa zai fuskanci matsala.
Hakan na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar ke shirin barin gidan gwamnati a farkon watan Nuwamba bayan rashin nasara a zaben da aka gudanar.
Ana zargin Shaibu zai mamaye gidan gwamnati
Kun ji cewa gwamnatin jihar Edo ta yi gargadi kan zargin mamayar gidan gwamnati da Philip Shaibu ke shirin yi.
Gwamna Godwin Obaseki ya ce har yanzu Shaibu korarren mataimakin gwamna ne, ba shi da wani tasiri a gwamnatin jihar.
Gwamnan ya bukaci babban sifetan yan sanda, Kayode Egbetokun da ya yi gaggawar daukar mataki kan Shaibu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng