PDP Ta Birkice, An Dakatar da Mataimakin Shugaban Jam'iyya Na Ƙasa
- Sabuwar matsala ta kunno kai a PDP da shugabannin gunduma suka dakatar da mataimakin shugaban jam'iyya na Kudu maso Gabas
- Shugabannin karkashin jagorancin Hebert Ovuta sun ce sun ɗauki wannan matakin saboda gano yana cin amanar jam'iyyar PDP
- Sai dai Chief Ali Odefa ya yi fatali da lamarin, ya ce waɗanda suka dakatar da shi ba ƴan jam'iyya PDP ba ne watau ba su da hurumi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Jam'iyyar PDP ta dakatar da mataimakin shugabanta na shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya, Chief Ali Odefa.
Shugabannin PDP na gundumar Ogudu Okwor da ke ƙaramar hukumar Onicha a jihar Ebonyi ne suka sanar da dakatar da Odefa a wani taron ƴan jarida a Abuja.
Leadership ta ruwaito cewa muƙaddashin shugaban PDP na gunduma, Hebert Ovuta ne ya sanar da dakatar da babban jigon jam'iyyar kan zargin cin amana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ovuta ya bayyana cewa dakatarwar ta yi daidai da tanadin sashe na 57 (3) na kundin tsarin mulkin PDP.
Meyasa PDP ta dakatar da Ali Odefa?
Mista Hebert Ovuta, wanda sauran shugabannin jam'iyyar PDP na gumdumar ke gefensa a lokacin da yake hira da ƴan jarida, ya ce:
"Mun zo nan ne domin sanar da ku matakin da kwamitin zartarwa na PDP a gundumar Ogudu-Okwor ya ɗauka na dakatar da Cif Ali Odefa, mataimakin shugaban PDP na shiyyar Kudu maso Gabas.
"Mun dakatar da shi bisa aikata cin amana da wasu laifuffuka da ake zarginsa da aikatawa waɗanda ke zubar da mutuncin PDP, hakan bai saɓawa kundin mulkin PDP ba."
"Bayan haka mun miƙa Cif Ali Odefa ga kwamitin ladabtarwa na jam'iyyar domin ɗaukar mataki na gaba," in ji Ovuta.
Shugaban PDP ya yi fatali da dakatarwar
Da yake mayar da martani kan lamarin, Cif Odefa ya yi watsi da hukuncin dakatar da shi da shugabannin gundumarsa suka yi.
A wata hira ta wayar tarho da Vanguard, Odefa ya ce wadanda suka fito a gaban ƴan jarida suna ɓaɓatun dakatar da shi ba ƴan PDP ba ne.
Zanga-zanga ta ɓarke a sakatariyar PDP
A wani rahoton kuma an samu ɓarkewar zanga-zanga a sakatariyar jam'iyyar PDP ta Rivers da ke a birnin Port-Harcourt watau babban birnin jihar.
Zanga-zangar ta ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoban 2024 ta ɓarke ne domin nuna adawa da shirin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng