Gwamna da Mutane Sun Yiwa Ƴan Sanda Ihu, Sun Kore Su daga Ofishin Hukumar Zabe
- Gwamna Siminalayi Fubara da wasu dandazon mutane sun kunyata ƴan sanda da aka tura ofishin hukumar zaɓe ta jihar Ribas
- Rahoto ya ce bayan gwamna ya ruguza shirin ƴan sandan, wasu mutane sun kore su daga ofishin RIISIEC tare da yi masu ihu
- Wannan dai na zuwa ne bayan rundunar ƴan sanda ta ce ba za ta shiga harkokin zaɓen kananan hukumomin da ake shirin yi ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Ƴan sandan da aka tura domin samar da tsaro a ofishin hukumar zaɓe ta jihar Ribas (RISIEC) sun baro wurin bisa tilas.
Rahotanni sun bayyana cewa dandazon mutanen da ke wurin ne suka fatattaki dakarun ƴan sandan yayin da ake shirye-shiryen zaɓen kananan hukumomi a gobe.
Meyasa aka tura ƴan sanda ofishin RISIEC?
The Nation ta tattaro cewa babu wanda ya san wanda ya tura ƴan sanda zuwa ofishin hukumar zaɓen saboda rundunar ƴan sanda ta ce ba za ta shiga lamarin ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani faifan bidiyo da ake yaɗawa ya nuna lokacin da mutanen wurin suka kama yiwa ƴan sandan ihu, suna kiransu da sunaye daban-daban kamar 'ɓarayi' da sauransu.
Ƴan sandan sun isa ofishin hukumar zaɓen da ke Fatakwal a cikin motocin sintiri amma ba su jima ba suka bar wurin sakamakon ihun da mutane suka fara masu.
Gwamna Fubara ya dura hukumar zabe
An tattaro cewa jim kaɗan bayan haka ne Gwamna Siminalayi Fubara da ƙusoshin gwamnati da wasu ƴan majalisar dokokin Ribas suka dura harabar ofishin.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan ya fitar, ya ce Fubara ya yi nasarar daƙile yunƙurin ƴan sanda na kwace iko da ofishin hukumar RISIEC da tsakar daren Jumu'a.
PDP da APC sun tararwa Gwamna Fubara
A wani labarin na daban Gwamna Siminalayi Fubara na fuskantar matsala daga jam'iyyun PDP da kuma APC kan zaben ƙananan hukumomi.
Jam'iyyun guda biyu sun kalubalanci gwamnan kan shirin gudanar da zaben a ranar 5 ga watan Oktoban 2024 duk da hukuncin da kotu ta zartar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng