'Yan Sanda Sun Ɗauki Matakin Juyawa Gwamna Baya a Gobe Zaben Kananan Hukumomi
- Rundunar ƴan sanda ta ce za ta yi biyayya ga umarnin kotun tarayya game da zaɓen kannaan hukumomin da ake shirin yi a Ribas
- Wannan mataki ne zuwa ne bayan zanga-zangar da ƴan PDP suka yi ranar Alhamis, inda suka nemi a yiwa hukuncin kotu ɗa'a
- Duk da nesanta kanta da zaben, rundunar ƴan sandan ta tabbatarwa al'umma cewa za ta sauke nauyinta na tabbatar da doka da oda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Rundunar ƴan sanda reshen Ribas ta bayyana cewa ba za ta shiga harkokin zaɓen kananan hukumomin da ake shirin yi a jihar ba.
Rundunar ta tabbatar da cewa za ta yi biyayya ga hukuncin babbar kotun tarayya, wadda ta hana jami'an tsaro shiga harkokin zaɓen na ranar Asabar, 5 ga watan Oktoba.
Ƴan PDP sun yi zanga-zanga a Rivers
Rahoton The Nation ya nuna wannan mataki da ƴan sanda suka ɗauka na zuwa ne sa'o'i 24 bayan zanga-zangar da ta gudana karkashin jagorancin PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu zanga-zangar sun buƙaci rundunar ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro su bi umarnin kotu, su tsame kansu daga duk abin da ya shafi zaɓen.
Ƴan sanda sun kafa hujja da hutuncin kotu
Kakakin ƴan sandan Ribas, Grace Iringe-Koko ta tabbatar da matakin da rundunar ta ɗauka na bin umarnin kotu a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis.
A cewar Iringe-Koko, sashen kula da harkokin shari'a na rundunar ƴan sanda ne ya bada shawarar ka da jami'ai su shiga zaɓen saboda hukuncin kotu ya fara aiki.
Vanguard ta rahoto Iringe-Koko na cewa:
"Ranar 30 ga Satumba, 2024, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin da ya sake haramtawa rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro shiga zaben kananan hukumomi a Ribas.
"Wannan ya sa sashen shari'a ya ba rundunar ƴan sandan shawarar kaucewa zaben tun da hukuncin kotun ya fara aiki."
Ƴan Fubara sun fara barin PDP daf da zabe
Rahotanni sun nuna kantomomin da Gwamna Siminalayi Fubara ya nada sun fara barin jam'iyyar PDP zuwa APP mai adawa a jihar Ribas.
Hakan na zuwa ne bayan jita-jita ta fara yawo cewa shi kansa gwamna yana shirye-shiryen sauya sheƙa saboda rikicinsa da Nyesom Wike.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng