‘Ni Zan Dama Yadda Za a Sha kan Zaɓen 2027’, Gwamna Ya Karfafa Tasirinsa

‘Ni Zan Dama Yadda Za a Sha kan Zaɓen 2027’, Gwamna Ya Karfafa Tasirinsa

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya shawarci masu neman kujerarsa da su kasance masu hakuri da juriya kan lamarin
  • Makinde ya ce tabbas zai taka rawa wurin zaben wanda zai gaje shi inda ya ce hakan ba yana nufin shi zai yi komai ba
  • Gwamnan ya bukaci masu sha'awar gadon kujerarsa da su yi hakuri saboda sai lokacin zaben za su san matsayarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya yi magana kan siyasar jihar da kuma zaben 2027.

Gwamnan ya ce zai taka muhimmiyar rawa wurin zaben dan takarar da zai gaje shi a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

Gwamna ya yi magana kan dan takararsa a zaben 2027
Gwamna Seyi Makinde ya ja kunnen masu neman kujerarsa a zaben 2027. Hoto: Seyi Makinde.
Asali: Facebook

Gwamna ya magantu kan magajinsa a 2027

Makinde ya bayyana haka ne a yau Alhamis 3 ga watan Oktoban 2024 a birnin Ibadan, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bayyana tasirin zaben inda ya nuna muhimmancin al'umma game da wanda zai kasance magajinsa.

Ya ce ba dole ba ne ya kasance mai iko gaba daya kan wanda zai gaje shi amma zai yi matukar taka rawa a lamarin.

"Zan ba da gudunmawa sosai wurin zaben wanda zai gaje ni duk da ba zai kasance ni ne mai iko gaba daya ko yanke hukuncin karshe ba."

- Seyi Makinde

2027: Gwamna Makinde ya ba yan siyasa shawara

Makinde ya shawarci masu neman gadon kujerarsa da su kasance masu hakuri da juriya, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Gwamnan ya ce dole wanda ya kamata ya gaje shi zai san makomarsa ne ana daf da zaben 2027 saboda wasu dalilai na musamman.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan PDP ya fadi umarnin mahaliccinsa kan takara a zaben 2027

Gwamna Makinde ya nemi yafiyar tsohon gwamna

Kun ji cewa Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce ba shi da wata matsala da tsohon gwamna, Rahidi Ladoja musamman a siyasance.

Makinde ya ce tarihin siyasarsa ba za ta taɓa cika ba sai da saka hannun tsohon gwamnan watau Baba Rashidi Ladoja.

Gwamnan ya bayyana haka ne a gidan Ladoja da ke birnin Ibadan a Oyo yayin bikin murnar cikan dattijon shekaru 80.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.