Ighodalo: Sabuwar Zanga Zanga Ta Ɓarke a Hedkwatar Hukumar INEC, Bayanai Sun Fito

Ighodalo: Sabuwar Zanga Zanga Ta Ɓarke a Hedkwatar Hukumar INEC, Bayanai Sun Fito

  • Ƴaƴan PDP a jihar Edo sun mamaye ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC da ke Benin kan sakamakon zaɓen gwamna
  • Masu zanga-zangar sun bukaci INEC ta soke nasarar da jam'iyyar APC ta samu a zaɓen da aka yi ranar 21 ga watan Satumba, 2024
  • A cewarsu, ɗan takarar PDP, Asue Ighodalo ne ya samu nasara a zaɓen da aka kammala ba Sanata Monday Okpebholo na APC ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Wasu gungun ƴaƴan jam'iyyar PDP a Edo sun fito zanga-zanga a hedkwatar hukumar zaɓe watau INEC ta jihar da ke Benin City.

Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga-zangar sun buƙaci INEC ta soke sakamakon zaben da ta bayyana wanda ya ba APC nasara a zaben da aka yi.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Ganduje da APC sun gamu da cikas ana dab da zabe

Dan takarar PDP a zaben Edo, Asue Ighodalo.
Ighodalo: Ƴaƴan PDP sun durfafi ofishin INEC na jihar Edo kan nasarar APC a zaɓen gwamna Hoto: Asue Ighodalo
Asali: Twitter

Magoya bayan jam'iyyar sun sake nanata cewa ɗan takararsu na PDP, Asue Ighodalo ne ya lashe zaɓen ba Monday Okpebholo na APC ba, Channels tv ta kawo labarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaɓen Edo: Sakamakon da INEC ta sanar

Idan za ku iya tunawa hukumar INEC ta ayyana Okpebholo na APC a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen ranar 21 ga watan Satumba da kuri'u 291,667.

Sakamakon da INEC ta sanar ya nuna ɗan takarar APC ya lallasa Ighodalo na PDP mai mulki a Edo wanda ya tashi da ƙuri'u 247,274 da Olumide Akpata na LP mai ƙuri'u 22,763.

Sai dai Ighodalo da Akpata sun yi fatali da sakamakon zaben, inda suka zargi APC da sayen kuri’u, kuma tuni jam'iyyar ta musanta wannan zargi.

Jam'iyyar PDP ya sha alwashin kalubalantar sakamakon zaɓen a gaban kotu. yana mai cewa shari'a za ta dawo masa haƙƙinsa da aka ƙwace.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta ba zabaɓben gwamnan jihar Edo takarda shaida, bayanai sun fito

Ƴaƴan PDP ba su amince da nasarar APC ba

Amma a yau Talata, 2 ga watan Oktoba, magoya bayan PDP sun fantsama zanga-zangar nuna adawa da nasarar APC, rahoton Leadership.

Masu zanga-zangar dai sun buƙaci INEC ta soke sakamakon da ta bayyana, inda suka jaddada cewa PDP ce ta samu nasara ba APC ba.

Tinubu ya gana da zaɓaɓɓen gwamnan Edo

A wani labarin kuma Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin zababben gwamnan Edo, Monday Okpebolo da mataimakinsa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaba Tinubu ya buƙaci Sanata Okpebholo da abokin aikinsa Dennis Idahosa su kulle kunnuwansu daga ƴan hayaniya, su yi wa nutanen Edo aiki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262