Dan Jam'iyyar PDP Ya Sauya Sheka Zuwa APC a Zauren Majalisar Tarayya
- Jam'iyyar PDP mai adawa a ƙasar nan ta rasa ɗaya daga cikin ƴan majalisun da take da su a majalisar wakilan Najeriya
- Ɗan majalisa mai wakiltar Ukwa ta Gabas/Ukwa ta Yamma daga Abia, Chris Nkwonta ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC
- Bayan sauya sheƙarsa zuwa APC mai rinjaye, shugaban majalisar tarayyar ya naɗa shi a matsayin shugaban wani kwamiti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ɗan majalisar wakilai, Chris Nkwonta ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC mai rinjaye.
Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ya sanar da sauya sheƙar Chris Nkwonta a zauren majalisar a ranar Laraba.
Ɗan majalisar PDP ya koma APC
Chris Nkwonta yana wakiltar mazabar tarayya ta Ukwa ta Gabas/Ukwa ta Yamma daga jihar Abia, cewar rahoton jaridar The Cable
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mambobin jam'iyyar APC a majalisar sun nuna farin cikinsu bayan sanarwar da aka yi na sauya sheƙarsa zuwa APC.
Ƴan adawa suna rashin amincewarsu
Sai dai, mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Aliyu Madaki, ya nuna rashin amincewarsa da sauya sheƙar.
Da yake kafa hujja da sashe na 68 na kundin tsarin mulkin ƙasar nan, Aliyu Madaki ya ce ɗan majalisa zai iya ficewa ne kawai daga jam’iyyar da ta ɗauki nauyin zaɓensa idan aka samu rikici a cikinta.
Sai dai, shugaban majalisar ya yi watsi da batun nasa, inda ya ce akwai rikici a PDP, rahoton jaridar Independent ya tabbatar.
"Bayanan da nake da su sun nuna akwai wani ɓangare a PDP."
- Tajudeen Abbas
Daga bisani shugaban majalisar ya ayyana Chris Nkwonta a matsayin shugaban kwamitin majalisar kan hukumar ci gaban yankin Kudu maso Gabas.
Mambobin APC sun koma PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar PDP a jihar Ondo ta karɓi masu sauya sheƙa daga APC a ranar Litinin, 30 ga watan Satumban 2024.
Jam’iyyar PDP ta yi maraba da tsohon shugaban hukumar raya yankin Neja-Delta, Dakta Benson Enikuomehin, tare da magoya bayansa sama da 200 zuwa cikin ta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng