Gwamna Ya Ƙara Takaita PDP, Ƴan Siyasa Sama da 200,000 Sun Koma APC

Gwamna Ya Ƙara Takaita PDP, Ƴan Siyasa Sama da 200,000 Sun Koma APC

  • Gwamnan Kaduna, Uba Sani ya yi ikirarin cewa ƴaƴan PDP sama da 200,000 sun sauya sheka zuwa APC musamman a kudancin jihar
  • Uba Sani ya ce sauya shekar wata babbar alama ce da ke nuna yadda al'umma suka ganmsu da salon gwamnatinsa na gaskiya da adalci
  • Gwamna Uba ya faɗi haka ne a wurin kaddamar da yaƙin neman zaɓen APC a zaɓen kananan hukumomin da za a yi a watan da muke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Yayin da ake shirye-shiryen zaɓen kananan hukumomi a Kaduna, ƴaƴan PDP sama da 200,000 sun koma APC musamman kudancin jihar.

Gwamna Uba Sani ne ya bayyana hakan, ya ce wannan babbar alama ce da ke nuna karɓuwar tsarin gwamnatinsa na yin adalci da daidaito.

Kara karanta wannan

"PDP ta mutu," Kwankwaso ya bayyana jam'iyyar da ta yunƙuro da ƙarfinta a Najeriya

Gwamna Uba Sani.
Gwamna Uba Sani ya yi ikirarin yaƴan PDP akalla 200,000 sun sauya sheka zuwa APC a Kaduna Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Facebook

Malam Uba Sani ya faɗi haka ne a wurin taron kaddamar da kamfen APC a Murtala Square da je cikin garin Kaduna kamar yadda ya sanar a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya faɗi alfanun sauya sheka zuwa APC

Gwamna Uba Sani ya ce sauya shekar ya nuna irin ci gaban da gwamnatinsa ta samu wajen tabbatar da adalci, daidaito da kuma gaskiya.

Uba Sani ya bayyana kwarin guiwarsa da nagartar ƴan takarar APC, yana mai cewa zai mara masu baya domin bunƙasa yankunan karkara.

Sani ya kuma haska irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fadin jihar Kaduna musamman ta fuskar farfado da yankunan karkara da samar da ababen more rayuwa.

Gwamna Uba Sani ya fara farfaɗo da karkara

Gwamna Sani ya ce tun da ya karɓi mulki, gwamnatinsa ta ba da fifiko ga ci gaban karkara, ya zuba ayyukan da suka hada da gina tituna 62 a fadin kananan hukumomi 23. 

Kara karanta wannan

1 ga Oktoba: Abin da ke faruwa a Kano bayan fara zanga zanga a wasu sassan Najeriya

Ya kara da cewa gwamnatinsa ta gina makarantun sakandire 60, sannan ta samar da isassun kayan aiki a firamare da sakandare sama da 200.

"An kusa fita daga wahala" - Gwamna Uba Sani

A wani rahoton kuma, Gwamna Uba Sani ya taɓo batun matsalolin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziƙi da suka addabi ƙasar nan.

Gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana cewa gwamnati na aiki tuƙuru domin kawo ƙarshen matsalolin nan ba da jimawa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262