"Na Shirya Rantsewa da Alƙur'ani Ban Taɓa Satar ko Kwabo ba," Tsohon Gwamna El Rufai
- Nasir El-Rufai ya ƙalubalanci tsofaffin gwamnonin Kaduna da sauran shugabanni, ya ce ya shirya rantsewa da Kur'ani bai yi sata ba
- Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya ce bai shiga harkar siyasa domin neman kudi ba, ya shiga ne da nufin yi wa al'ummarsa aiki
- Majalisar dokokin Kaduna tana zargin gwamnatin El-Rufai da yin sama da fadi da N423bn a shekaru takwas da ya yi da yake mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce ya shiga siyasa ne don ya yi wa jama’a hidima, ba don neman kudi ko satar dukiyar talakawa ba.
Malam Nasir El-Rufai ya ƙara da cewa ya gamsu da abubuwan da ya yi a siyasa tun kafin ya zama gwamnan jihar Kaduna a 2015.
Ya bayyana haka ne a wani shirin Hausa da aka watsa a gidan rediyon Freedom da ke Kaduna a safiyar ranar Talata, 1 ga watan Oktobo, Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar Kaduna na zargin gwamnatin El-Rufai
Idan ba ku manta ba majalisar dokokin jihar Kaduna na zargin gwamnatin El-Rufai da karkatar da sama da Naira biliyan 423 cikin shekaru takwas da ya yi yana mulki.
Tsohon gwamnan da sauran abokan aikinsa sun musanta zarge-zargen satar kuɗin al'umma, inda suka ce gwamnatin jihar da majalisa na masu bi-ta da ƙulli.
Da yake jawabi a shirin, El-Rufai ya ce a shirye yake ya rantse da Alƙur’ani a duk lokacin da tsofaffin gwamnonin Kaduna da shugabannin yanzu suka rantse ba su saci ko sisi ba.
"Na shirya ratsewa da Alƙur'ani," El-Rufai
"Na yi shiru ne don naga yadda abubuwan za su kasance, amma ni dai ina ƙara godewa Allah da rokonsa ya taimake ni saboda ni ɗan adam ne, a koda yaushe ina kokarin kaucewa aikata laifi ko cin amanar jama'a.
"Ina yawan faɗa idan har tsofaffin gwamnonin Kaduna da sauran shugabanni za su rantse da Alƙur'ani ba su taba ɗaukar kuɗin al'umma ba, nima a shirye nake na rantse.
"Saboda na san ban shiga siyasa don na saci kuɗin jama'a ba, na shiga siyasa ne domin na yiwa al'ummar Kaduna aiki, ba kuɗi na zo nema ba, ina ƙara gode Allah, na gamsu da abubuwan da na yi tun kafin zama gwanna.
- Malam Nasiru El-Rufai.
Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa a yanzu ana zarginsa na karkatar da wasu kuɗi ba tare da faɗin a ina kudin suka ɓata ko wanda ya sace su ba.
Uba Sani ya musanta raba gari da El-Rufai
A wani labarin kuma gwamnan Kaduna, Uba Sani ya musanta rade-radin da ake yadawa cewa ya na yi wa tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai bi-ta-da-kulli.
Uba Sani ya ce tun 1999 ya ke da alaka mai kyau da dukkanin tsofaffin gwamnonin jihar kuma bai ware Malam Nasir El-Rufai ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng