Ana Murnar Ranar Ƴancin Kai, An Buƙaci Shugaba Tinubu Ya Kori Wani Minista
- Jigon PDP, Dare Glintstone Akinniyi ya buƙaci Bola Ahmed Tinubu ya kori ministan Abuja, Nyesom Wike saboda ya cika surutu
- Akinniyi ya yaba da ƙoƙarin wasu ministoci uku, inda ya ce sama da kaso 80% na muƙarraban shugaban ƙasa sun cancanci a sallame su
- A wata hira da Legit.ng ranar Litinin, jagoran PDP ya ba shugaban ƙasa shawarar yadda ya kamata ya yi gyara a majalisar zartaswa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Mai magana da yawun ƙungiyar matasan PDP ta kasa, Dare Glintstone Akinniyi ya roƙi shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya tsige ministan Abuja, Nyesom Wike.
Akinniyi ya ba da shawarar a sallami Wike ne yayin da yake tsokaci kan shirin shugaba Tinubu na yin garambawul a majalisar zartaswansa.
Wane dalili zai sa Tinubu ya kori Ministan Abuja?
A wata hira da Legit.ng ranar Litinin, 30 ga watan Satumba, 2024, Mista Akinniyi ya ce Wike ya jingine aikinsa na ministan Abuja, ya maida hankali kan siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma bayyana cewa surutun Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ya fi aikinsa yawa, yana jawowa gwamnati mai ci abin magana.
Akinniyi ya roƙi Tinubu kada ya kuskure ya kori ministoci uku, ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ministan ayyuka, Dave Umahi da ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo.
A cewarsa, in ban da waɗannan mutanen uku da ya ambata a sama, ya kamata shugaban ƙasa ya sallami dukkan sauran ministocin ya yi sabon zubi.
Akinniyi ya jero ministoci 3 da suka yi ƙoƙari
Jigon PDP ya ce:
"Da farko dai ina ba da shawarar a kori ministan Abuja, ya kawo hayaniya da surutu a wannan gwamnatin, riƙe mutum kamar Nyesom Wike bai dace ba."
"Ministoci uku da suka haɗa da na harkokin cikin gida, ayyuka da sufurin jiragen sama sun yi zarra, amma ba ya ga su, duk a kori sauran."
Ranar ƴanci: Tinubu ya ɗauki alƙawari
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya ƙara tabbatarwa ƴan Najeriya duk wahalar da suke kuka a kai za ta wuce kuma daɗi na nan tafe.
Shugabar ƙasar ya bayyana ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi domin abinci ya wadata da kuma rage farashinsa a faɗin ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng