"PDP Ce Sila," Jam'iyyar APC Ta Bayyana Muhimmin Aikin da Ya Cinye Shekarun Mulkin Buhari

"PDP Ce Sila," Jam'iyyar APC Ta Bayyana Muhimmin Aikin da Ya Cinye Shekarun Mulkin Buhari

  • Jam'iyyar APC ta ce gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ta shafe shekara takwas tana share ɓarnar PDP ta shekara 16
  • Sakataren watsa labaran APC, Felix Morka ya ce ba karamar illa PDP ta yiwa ƙasar nan ba daga 1999 zuwa 2015
  • Morka ya yi kira ga ƴan Najeriya su ƙara hakuri da Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce za ta cika alƙawurran da ta ɗauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Sakataren watsa labaran APC na ƙasa, Felix Morka ya kare gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Morka ya bayyana cewa Buhari ya shafe tsawon shekaru takwas a mulki yana share datti da tsaftace kura-kuran da gwamnatin PDP ta tafka na tsawon shekara 16.

Kara karanta wannan

Badakalar N27bn: EFCC ta sa lokacin gurfanar da tsohon gwamna gaban kotu

Muhammadu Buhari.
APC ta ce ba ƙaramar illa PDP ta yiwa Najeriya a shekaru 16 da ta yi tana mulki ba Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Felix Morka ya yi wannan furucin ne a shirin siyasa na yau na gidan talabijin din Channels tv ranar Litinin, 30 ga watan Satumba, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'PDP ya jawo wahalar rayuwa a Najeeiya'

Muhammadu Buhari ya karbi mulki a 2015 daga hannun PDP, wacce ta shafe shekaru 16 tana jan ragamar Najeriya tun bayan daowar mulkin demokuraɗiyya a 1999.

Amma kakakin APC na ƙasa ya ce duk wannan wahalar da ake sha a ƙasar nan ta samo asali ne daga gurbataccen mulkin PDP da a yanzu gwamnatin APC ke ƙoƙarin gyarawa.

Wane aiki gwamnatin Buhari ta yi a shekara 8?

Felix Morka ya ce:

"Babu abin da gwamnatin Buhari ta yi a cikin shekaru takwas, illa tsaftacewa tare da kawar da barnar da PDP ta yi.
"Abin ƴan Najeriya ba su sani ba shi ne PDP ta yiwa tattalin arziki lahani ta hanyar fitar da miliyoyin Daloli da sunan yin ayyukan raya ƙasa amma duka kudin sun zarce aljihunan wasu..

Kara karanta wannan

Tinubu ya raba N3.5bn ga malamai, likitoci da sauransu, bayanai sun fito

Saboda haka shi Buhari wata gwamnati ce mai shiga tsakani da ta kawo ɗauki ta riƙe Najeriya sannan ta tsamo ta daga rami.

Felix Morka ya yi kira ga ƴan Najeriya su kara hakuri da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu wadda a cewarsa za ta cika alkawuran da ta dauka.

Najeriya ta roƙi China ta yafe mata bashi?

Kuna da labarin gwamnatin tarayya ta ce ba a tattauna batun yafewa Najeriya bashi ba a ganawar Bola Tinubu da shugaban China, Xi Jinping.

Ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Tuggar ne ya bayyana hakan, ya ce China a shirye take ta ba Najeriya ƙarin bashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262