EFCC Ta Gurfanar daTsohon Gwamna a Arewa kan Tuhumar 'Sace' N27bn

EFCC Ta Gurfanar daTsohon Gwamna a Arewa kan Tuhumar 'Sace' N27bn

  • Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku da tsohon babban sakatare a gaban kotun tarayya
  • EFCC ta shigar da ƙarar mutanen biyu ne kan tuhume-tuhume 15 da suka kunshi zamba cikin aminci, haɗa baki da satar N27bn
  • Waɗanda ake zargin dai sun musanta tuhumar da ake yi masu, alkali ya umarci EFCC ta ci gaba da tsare su zuwa zama na gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hukumar yaƙi da rashawa watau EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku a babbar kotun Abuja kan tuhumar zamba.

EFCC ta gurfanar da Ishaku tare da tsohon babban sakataren ma'aikatar kananan hukumomi da sha'anin masarautu a Taraba, Bello Yero gaban mai shari'a Sylvanus Oriji

Kara karanta wannan

"PDP ce sila," APC ta bayyana muhimmin aikin da ya cinye shekarun mulkin Buhari

Tsohon gwamnan Taraba, Darius Ishaku.
EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan Taraba da babban sakarare a gaban kotu Hoto: Darius Ishaku
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Litinin, 30 ga watan Satumba, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC ta shigar da tuhume-tuhume 15

EFCC ana tuhumar mutanen biyu da aikata laifuffuka 15 da suka ƙunshi zamba cikin aminci, haɗa baki da karkatar da N27bn.

Ana tuhumar tsohon gwamnan da haɗa baki da tsohon babban sakataren wajen sace dukiyar talakawa a lokacin da yake matsayin gwamna tsakanin 2015-2019.

Sai dai bayan karanta masu dukkan tuhume-tuhume 15, waɗanda ake ƙara sun musanta aikata ko ɗaya daga cikin laifuffukan.

An nemi belin tsohon gwamna

Bisa wannan ne lauyan EFCC, Rotimi Jacobs ya roki kotu ta sa ranar fara shari'a ko ta yi hanzari ta ƙarkare shari'ar domin tabbatar da laifi ko akasin haka kan waɗanda ake tuhuma.

Kara karanta wannan

Matawalle: EFCC ta tabo batun bincikar tsohon gwamnan Zamfara

A nasu ɓangaren, lauyan Darius Ishaku, Paul Haris Ogbole da lauyan Bello Yero, Oluwa Damilola Kayode sun shigar da buƙatar bayar da belin waɗanda ake ƙara.

Kotu ta ɗage zaman shari'ar EFCC

Mai shari’a Oriji ya dage sauraron karar zuwa ranar Alhamis, 3 ga watan Oktoba, domin yanke hukunci kan buƙatar neman belin Ishaku da Bello.

Haka nan kuma alkalin ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake tuhuma a hannun EFCC.

EFCC za ta ɗauko fayil din Matawalle

A wani rahoton kuma hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa za ta yi bincike kan zargin da ake yi wa Bello Matawalle.

EFCC ta bayyana cewa za ta binciki zargin da ake yi wa tsohon gwamnan na Zamfara kan karkatar da kuɗin jihar lokacin ya na mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262