Zaben Ondo: Ganduje da APC Sun Gamu da Cikas Ana Dab da Zabe

Zaben Ondo: Ganduje da APC Sun Gamu da Cikas Ana Dab da Zabe

  • Jam'iyyar APC ta samu koma baya a jihar Ondo gaban zaɓen gwamnan jihar da ke tafe a watan Nuwamban 2024
  • Dubban magoya bayan APC a ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP mai adawa a jihar
  • Alhaji Yusuf Abdulateef wanda ya jagorancesu zuwa jam'iyyar PDP ya bayyana cewa sun fice daga APC ne saboda shugabanci mara kyau a jihar da Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Dubban mambobin jam’iyyar APC da ke mazaɓa ta ɗaya, a garin Ore, a ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar Ondo, sun sauya sheƙa zuwa PDP.

Mambobin na APC sun koma PDP ne a ranar Asabar a gabanin zaɓen gwamnan jihar da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Ganduje da APC sun yi babban kamu bayan dan majalisa ya koma jam'iyyar

Magoya bayan APC sun koma PDP a Ondo
Mambobin APC sun koma PDP a jihar Ondo Hoto: @OfficialAPCNg, @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta rahoto cewa masu sauya sheƙar sun koma PDP ne ƙarƙashin jagorancin wani jigon APC a yankin, Alhaji Yusuf Abdulateef.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Yusuf Abdulateef ya bayyana cewa sun fice daga jam'iyyar APC ne saboda shugabanci mara kyau a jihar Ondo da Najeriya.

Meyasa suka fice daga APC zuwa PDP?

Abdulateef ya bayyana cewa sauya sheƙar ya nuna cewa sun samu ƴanci daga ƙangi sannan ya yi alƙawarin yin aiki domin nasarar ɗan takarar gwamnan PDP, Honorabul Agboola Ajayi.

Ya kuma ba da tabbacin cewa ɗumbin magoya bayan APC a ƙaramar hukumar za su sauya sheƙa zuwa PDP kafin zuwa zaɓen gwamnan.

Ya bayyana cewa ya koma PDP ne tare da magoya bayansa a ƙaramar hukumar Odigbo waɗanda yawansu zai kai mutum 5,000.

Alhaji Yusuf Abdulateef ya bayyana cewa za su haɗa kai da mambobin PDP domin ceto jihar daga shugabanci mara kyau wanda ya jawo yunwa, tsadar rayuwa da talauci.

Kara karanta wannan

‘Yan Damfara ne,’: NNPP a Kano ta gargadi Barau kan karbar masu canza sheka

Kotu ta takawa APC da PDP burki

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun jihar Kano ta yi zama kan korafin jam'iyyun APC da PDP game da zaben kananan hukumomi.

Kotun ta dakatar da APC da PDP da kuma jam'yyu 19 daga hana hukumar zaben jihar (KANSIEC) karbar kudin fom din takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng