Minista Ya Fadi Wanda Ya Yi Sanadi Tinubu Ya ba Shi Mukami, Ya Jero Alherinsa

Minista Ya Fadi Wanda Ya Yi Sanadi Tinubu Ya ba Shi Mukami, Ya Jero Alherinsa

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike ya sake samun yabo na musamman a wurin karamin Ministan man fetur, Heineken Lokpobiri
  • Lokpobiri ya bayyana yadda Wike ya taka rawa ta musamman wurin tabbatar da ganin ya samun muƙamin Minista a gwamnatin Bola Tinubu
  • Ministan ya bayyana wasu muƙamai da tsohon gwamnan Rivers, Wike ya yi sanadi musamman a wannan gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Karamin Ministan man fetur, Heineken Lokpobiri ya yi magana kan mukamin da aka ba shi.

Lokpobiri ya ce Ministan Abuja, Nyesom Wike shi ya yi ruwa ya yi tsaki wurin ba shi wannan muƙamin.

Minista a gwamnatin Tinubu ya fadi wanda ya yi sanadin samun muƙamin
Karamin Ministan man fetur, Heineken Lokpobiri ya ce Nyesom Wike ne sanadin samun muƙaminsa na minista. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Hon. Heineken Lokpobiri.
Asali: Facebook

Lokpobiri ya yabawa Wike kan sanadin mukaminsa

Kara karanta wannan

'Wahala za ta kare', Minista ya fadi yadda Tinubu ke kokarin dakile halin kunci

Ministan ya bayyana haka ne a jiya Asabar 28 ga watan Satumbar 2024 a birnin Abuja yayin wani taro, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lokpobiri ya yabawa tsohon gwamnan Rivers inda ya ce ya taka rawa sosai wurin tabbatar da shi a matsayin Minista.

"Yana da muhimmanci ku sani, ni da na ke tsaye da ku a nan a matsayin karamin Ministan man fetur, Wike ne sanadi."
"Kun ji cewa babban mai kula da kudi na hukumar NDDC ma Wike ne sanadin mukaminsa."
"Tarihin samun muƙamin Minista na ya fara ne tun daga gidan Wike a birnin Port Harcourt wanda da yawanku ba ku sani ba."

- Heineken Lokpobiri

Muƙamin Lokpobiri a mulkin Muhammadu Buhari

Lokpobiri ya rike muƙamin Ministan noma da harkokin karkara a lokacin mulkin Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2019, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

"Wa ka taba ginawa": Tsohon gwamna ga yaronsa gwamnan PDP, ya bugi kirji

Daga bisani kuma Shugaba Bola Tinubu ya nada shi karamin Ministan man fetur a watan Agustan 2024 tare da Nyesom Wike wanda shi ne Ministan Abuja.

Wike ya kalubalanci yaronsa, Siminalayi Fubara

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Rivers, Barista Nyesom Wike ya kalubalanci Gwamna Siminalayi Fubara na jihar kan siyasa musamman a jihar.

Wike ya gotantawa Fubara inda ya ce shi ne ya yi sanadin kasancewarsa gwamna a jihar inda ya kalubalance shi da cewa ya nuna wani da ya taba ginawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.