Rigima Ta Yi Kamari da Gwamna Ya Zargi Mataimakinsa da Shirin Kutse a Gidan Gwamnati
- Mako daya bayan kammala zaben gwamnan Edo, gwamnatin jihar ta zargi mataimakin gwamna, Philip Shaibu da neman rigima
- Gwamnatin jihar ta zargi Shaibu ta shirya makarkashiya domin mamayar gidan gwamnati a ranar Litinin 30 ga watan Satumba
- Wannan na zuwa ne bayan kotu ta tabbatar da Shaibu a matsayin halastaccen mataimakin gwamnan jihar bayan tsige shi da aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya zargi mataimakinsa da neman mamayar gidan gwamnati.
Obaseki yana zargin Philip Shaibu zai mamayi gidan gwamnatin jihar a ranar Litinin 30 ga watan Satumbar 2024.
Obaseki ya zargi Shaibu bayan faduwa zabe
Hadimin gwamnan na musamman, Crusoe Osagie shi ya tabbatar da haka a jiya Asabar 28 ga watan Satumbar 2024, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Osagie ya shawarci Shaibu da ya yi gaggawar janye wannan kuduri na shi da zai kawo rigima da tashin hankali a jihar.
Ya roki sifetan yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun da ya tabbatar Edo ba ta tsunduma cikin fitina ba saboda kudurin Shaibu.
"Mu na jan hankalin babban sifetan yan sanda, Kayode Egbetokun game da nufin mataimakin gwamna, Kwamred Philip Shaibu."
"Shaibu na kokarin shiga gidan gwamnati karfi da yaji domin tabbatar da hukunci alkaln kotu."
- Crusoe Osagie
Obaseki ya fadi illar da Shaibu ya yi
Gwamnatin jihar ta ce lokacin da Shaibu ya yi kokarin aiwatar da irin haka sai a aka rasa ran jami'in dan sanda a jihar wanda hakan abin takaici ne.
Ta tabbatar da cewa dole a kare faruwar hakan a nan gaba saboda wannan karo za a iya rasa rayuka da dama.
Gwamna ya yi rashin nasara a kotu
Kun ji cewa bayan rashin nasara a zaben gwamnan jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki ya sake samun matsala a kotu kan sha'anin gona.
Jigon APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu shi ya maka gwaman a kotu da zargin kwace masa gonaki ba tare da ka'ida ba a jihar.
Alkalin kotun, Peter Akhihiero ya yi fatali da matakin da gwamnan ya dauka na kwace gonakin Ize-Iyamu a karamar hukumar Oredo.
Asali: Legit.ng