Rikicin Rivers: Gwamnan PDP Ya Ba Wike da Gwamna Fubara Shawara

Rikicin Rivers: Gwamnan PDP Ya Ba Wike da Gwamna Fubara Shawara

  • Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri a ranar Asabar, ya ziyarci jihar Rivers domin halartar wani muhimmin taro
  • A cikin wani faifan bidiyo, Gwamna Fintiri ya halarci wajen gagarumar liyafar da aka shirya domin karram ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike
  • Dangane da rikicin siyasar Rivers, Gwamna Fintiri ya buƙaci Wike da Gwamna Sim Fubara da su kawo ƙarshen ɓarakar da ke tsakaninsu domin ci gaban jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya yi magana kan rikicin siyasar jihar Rivers.

Gwamna Fintiri ya roƙi ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da su kawo ƙarshen rikicin siyasar jihar.

Kara karanta wannan

Ganduje da APC sun yi babban kamu bayan dan majalisa ya koma jam'iyyar

Fintiri ya ba Wike da Fubara shawara
Gwamna Fintiri ya bukaci Wike da Fubara su sasanta Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Ahmad Fintiri
Asali: Facebook

Rikicin Rivers: Fintiri ya roƙi Wike da Fubara

Gwamna Fintiri ya yi wannan roƙon ne a ranar Asabar, 28 ga watan Satumba lokacin da ya halarci liyafar da shugaban ƙabilar Ijaw suka shirya domin karrama Wike, cewar rahoton TVC News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da alama gwamnan jihar na Adamawa yana cikin na kusa da Wike bayan wannan matakin da ya ɗauka a ranar Asabar.

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde da sauran tsoffin mambobin G-5, Ifeanyi Ugwuanyi (tsohon gwamnan jihar Enugu), Okezie Ikpeazu (tsohon gwamnan jihar Abia), da Samuel Ortom (tsohon gwamnan jihar Benue), sun halarci taron a ranar Asabar.

Hakan na zuwa ne bayan Fintiri ya nuna goyon bayansa ga Ambasada Umar Damagun a matsayin muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, wanda makusanci ne ga Wike.

Nuna goyon baya ga Damagum dai ya biyo bayan rashin jituwar cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Tsohon kwamishina ya caccaki Gwamna Dauda, ya ba shi shawara kan Matawalle

Kalli bidiyon jawabin Gwamna Fintiri a ƙasa:

Wike ya gana da kwamitin BoT na PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya gana da majalisar amintattu (BoT) na PDP karkashin jagorancin Sanata Adolphus Wabara a daren Talata, 17 ga watan Satumban 2024.

A watan Agusta, BoT ta rubutawa Nyesom Wike wasiƙa, inda suka nemi zama da shi don warware rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP musamman a jihar Rivers.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng