Ganduje da APC Sun Yi Babban Kamu Bayan Dan Majalisa Ya Koma Jam'iyyar

Ganduje da APC Sun Yi Babban Kamu Bayan Dan Majalisa Ya Koma Jam'iyyar

  • Jam'iyyar Labour Party (LP) ta rasa ɗan majalisarta wanda mamba ne a majalisar dokokin jihar Cross Rivers da ke yankin Kudu maso Kudu
  • Honarabul Odey Brian ya koma jam'iyyar APC mai mulki a jihar ne tare da magoya bayansa har mutum 2,000 bayan ya fice daga LP
  • Ya samu tarba daga manyan jiga-jigan APC a jihar da suka haɗa da Gwamna Bassey Otu, kwamishinoni da sauran manyan jami'an gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Cross Rivers - Ɗan majalisar dokokin jihar Cross Rivers mai wakiltar mazaɓar Yala 1, Honarabul Odey Brian ya koma jam'iyyar APC bayan ya fice daga jam'iyyar Labour Party (LP)

Ɗan majalisar ya yabawa Gwamna Bassey Otu na jihar bisa yadda ya kawo ci gaba a jihar.

Kara karanta wannan

Arewa na cikin matsala, ambaliya ta ƙara kashe mutum 29, gidaje 321,000 sun lalace

Dan majalisa ya koma APC a Cross Rivers
Dan majalisar jam'iyyar LP ya koma APC a jihar Cross Rivers Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

APC ta yi kamu a Cross Rivers

Ɗan majalisar ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron ficewarsa daga jam'iyyar Labour Party zuwa APC a mazaɓarsa ta Yahe cikin ƙaramar hukumar Yala ta jihar, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Honarabul Odey Brian ya koma APC ne tare da magoya bayansa mutum 2,000 da shugabannin LP na ƙaramar hukumar Yala da sauran ƙananan hukumomin shiyyar Cross Rivers ta Arewa.

Ɗan majalisar ya samu tarba

Ɗan majalisar ya samu tarba daga wajen shugaban APC na Yala wanda ya ba shi kwafi na kundin tsarin mulkin jam'iyyar da tarin tsintsiyoyi.

Taron ya samu halartar Gwamna Bassey Otu wanda shugaban majalisar dokokin jihar, Elvert Eyambem ya wakilta, shugaban APC na jihar, Alphonsus Ogar Eba Esq, mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar, Sylvester Agabi Jnr.

Sauran sun haɗa da shugaban ma'aikatan gwamnan jihar, Emmanuel Ironbar, mataimakin shugaban ma'aikatan gwamnan jihar Boniface Okache da sauran manyan ƙusoshin gwamnati.

Kara karanta wannan

Kungiyar NLC ta tsunduma yajin aiki, an samu bayanai

APC ta dakatar da tsohon kakakinta a Kwara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta dakatar da tsohon sakataren yaɗa labaranta, Alhaji Tajuedeen Aro a jihar Kwara.

Shugabannin jam'iyyar na Ojomu ta Arewa maso Yamma sun zargi tsohon kakakin APC da cin amana da zagon ƙasa, shiyasa suka dakatar da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng