Damagum: Malami Ya Hango Gwamnan da Zai Fice daga PDP zuwa Wata Jam'iyya

Damagum: Malami Ya Hango Gwamnan da Zai Fice daga PDP zuwa Wata Jam'iyya

  • Primate Elijah Ayodele ya bayyana cewa wani gwamnan PDP zai sauya sheka zuwa wata jam'iyar nan ba da daɗewa ba
  • Babban malamin cocin ya ce matuƙar Umar Damagum zai ci gaba da jan ragamar PDP, to jam'iyyar ba za ta kai labari ba
  • Ayodele ya kuma bayyana mutum biyu da yake ganin ɗayansu ne kaɗai zai iya ceto PDP daga ramin da ta faɗa a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jagoran cocin INRI Evangelical na ƙasa, Primate Elijah Ayodele ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba jam'iyyar PDP za ta rasa ɗaya daga cikin gwamnoninta.

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Osho Oluwatosin ya fitar, malamin cocin ya ce gwamnan zai sauya sheka zuwa wata jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Tinubu na shirin garambawul, wani jigo ya yi magana kan ministocin da za a kora

Primate Ayodele.
Primate Ayodele ya ce nan ba da daɗewa ba gwamnan PDP zai sauya sheka zuwa wata jam'iyya Hoto: Primate Elijah Ayodele
Asali: Facebook

Ayodele ya buƙaci a tsige Damagum a PDP

Primate Ayodele ya yi gargaɗin cewa shugabannin PDP na yanzu ba za su iya komai ba, idan kuma aka barsu jam'iyyar za ta mutu murus kafin zaɓen 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fitaccen limamin cocin ya bayyana cewa PDP ta kai gargara kuma matuƙar ba a ɗauki mataki ba to za ta zama tarihi, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Ayodele ya ce tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark ko Gabriel Suswam ne kaɗai za su iya ceto jam'iyyar daga dogon suman da ta yi.

PDP za ta rasa gwamna nan kusa

"Nan ba da dadewa ba PDP za ta rasa gwamna saboda a halin yanzu jam’iyyar ta kai gargara, in dai Damagum ne shugaba, PDP ba za ya iya cin zaɓe ba.
"Ku zabi tsakanin Gabriel Suswam da David Mark, kowane a cikinsu zai iya tunkarar kowace jam'iyyar siyasa, ta kowace hanya za su iya farfaɗo da PDP ta dawo kan ganiyarta.

Kara karanta wannan

Edo: Jonathan ya fadi hanyar da za a magance maguɗin zabe a Najeriya

"Duk wanda ku ka ɗauka daga cikin mutum biyun da na ambata zai iya ceto PDP daga ramin da ta faɗa, idan ƴaƴan PDP suka ba su goyon baya, za su samu nasara."

- Primate Ayodele.

Ayodele ya shawarci PDP ta kafa kwamitin sasanci idan tana son ta farfaɗo saboda sai an yi aiki tuƙuru idan ana son babbar jam'iyyar ta dawo kan ganiyarta a 2027, PM News ta tattaro.

Gwamnonin PDP da ke son tsige Damagum

A wani labarin kuma an ji kishin-kishin gwamnonin PDP sun raba gari kan bukatar Umar Damagum ya ci gaba da zama shugaban jam’iyyar na kasa.

Ambasada Damagum ya maye gurbin Iyorchia Ayu a cikin Maris 2023, sai dai a yanzu yana fuskantar barazanar sauke shi daga wannan mukami.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262