Abin da Shugaba Tinubu Ya Faɗawa Zababben Gwamnan Edo da Jagororin APC a Aso Villa

Abin da Shugaba Tinubu Ya Faɗawa Zababben Gwamnan Edo da Jagororin APC a Aso Villa

  • Bola Ahmed Tinubu ya karɓi bakuncin zababben gwamnan Edo, Monday Okpebolo da mataimakinsa a fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • Shugaba Tinubu ya buƙaci Sanata Okpebholo da abokin aikinsa Dennis Idahosa su kulle kunnuwansu daga ƴan hayaniya, su yi wa nutanen Edo aiki
  • Shugaban APC, Abdullahi Ganduje da wasu gwamnonin jam'iyyar ne suka jagoranci zabaɓɓun zuwa Aso Villa domin gabatar da su ga Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya buƙaci zababben gwamnan Edo, Sanata Monday Okpebolo, da ya ba da fifiko ga ci gaban jihar.

Shugaban ƙasar ya tabbatar masa da cewa zai samu cikakken goyon bayan gwamnatin tarayya da kuma kungiyar gwamnonin APC.

Kara karanta wannan

Ganduje, zababben gwamnan Edo da gwamnonin APC sun shiga ganawa da Tinubu

Shugaban kasa Bola Tinubu.
Shugaba Tinubu ya bukaci zababben gwamnan Edo ya yi wa al'ummarsa aiki Hoto: @OfficialABAT
Asali: Facebook

Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin jagororin APC a Aso Villa, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje da gwamnonin APC ne suka ɗauki zaɓaɓɓen gwamnan da mataimakinsa, Dennis Idahosa zuwa wurin Tinubu.

Tinubu ya ja hankalin zababben gwamnan Edo

Bola Tinubu ya ja hankalin zaɓaɓɓen gwamnan kan muhimmancin shugabanci na gari da kuma kyautatawa al'ummar jihar Edo da suka ba shi amana.

"Zabaɓɓen gwamna, lokaci ya yi da za ka kawo sauyi da ci gaba, muna tare da kai, ka koya daga gwamnonin APC, ina da yaƙinin zaka iya.
"Ka samu nasara amma ka sani demokuraɗiyya ta na da kalubale musamman a kasashe masu tasowa da tattalin arziki irin namu."

Shugaba Tinubu ya ƙara taya su murna

Shugaba Tinubu ya ƙara taya zaɓaɓɓen gwamnan da mataimakinsa murna, inda ya ayyana su a matsayin wata alama da Allah ya kaddara masu yin aiki tare.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta ba zabaɓben gwamnan jihar Edo takarda shaida, bayanai sun fito

"Da farko kun fara a matsayin abokan hamayya yanzu kun kare a abokan aiki, wannan babban misali ne na fahimtar juna a siyasa," in ji shi.

Tinubu ya jinjinawa APC da INEC

A rahoton Punch, Tinubu ya yaba da rawar da tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole, gwamnonin APC da jagororin jam'iyya suka taka har Monday ya samu nasara.

Shugaban ya kuma jinjinawa INEC da jami’an tsaro bisa tabbatar da an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana, ba tare da samun rahoton tashin hankali ba.

An nemi Tinubu ya dakatar da Matawalle

A wani rahoton kuma wata ƙungiya a jam'iyyar APC ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Bello Matawalle daga muƙaminsa.

Ƙungiyar TYN ta shawarci Tinubu ya dakatar da ƙaramin ministan tsaron domin gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi masa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262