Hukumar INEC Ta Ba Zabaɓben Gwamnan Jihar Edo Takarda Shaida, Bayanai Sun Fito

Hukumar INEC Ta Ba Zabaɓben Gwamnan Jihar Edo Takarda Shaida, Bayanai Sun Fito

  • INEC ta ba zaɓaɓɓen gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo da mataimakinsa takardar shaidar lashe zaɓen da aka yi
  • Manyan kusoshin jam'iyya mai mulki ciki har da shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje sun halarci taron a hedkwatar INEC
  • A ranar Asabar da ta gabata 21 ga watan Satumba, 2024 aka gudanar da zaɓen gwamna a Edo, wanda a ƙarshe APC ta samu nasara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ba zababben gwamnan Edo, Sanata Monday Okpebholo da mataimakinsa, Dennis Idahosa takardar shaidar laashe zaɓe.

INEC ta ba waɗanda suka samu nasara takardar shaidar lashe zaɓen ne a wani ɗan kwarya-kwaryar taro da aka shirya a hedkwatar hukumar da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Ganduje, zababben gwamnan Edo da gwamnonin APC sun shiga ganawa da Tinubu

Zababben gwamnan Edo, Monday Okpebholo.
Hukumar INEC ta ba zababben gwamnan Edo shaidar lashe zabe Hoto: Monday Okpebholo
Asali: Twitter

Ganduje da ƙusoshin APC sun halarci taron

Rahoton Vanguard ya nuna shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da wasu ƴan kwamitin gudanarwa NWC sun halarci taron yau Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran waɗanda suka raka ɗan takarar APC karɓo takardar shaidar a INEC sun haɗa da mataimakin gwamnan Edo da aka maido, Philip Shaibu da Sanata Matthew Uroghide.

Janar Cecil Esekhaigbe (mai ritaya), Sanata Francis Alimikhena, Hon. Ogbeide Ihama, Hon. Omosede Igbinedion, Blessing Agbonmhere da wasu jiga-jigai sun halarci wurin.

Yadda APC ta lashe zaɓen Edo

INEC ta ayyana Okpebolo a matsayin wanda ya lashe zaben ranar Asabar, 21 ga watan Satumba da kuri'u 291,667 inda ya doke abokin karawarsa, Asue Ighodalo na PDP wanda ya samu kuri'u 247,274.

Olumide Akpata na jam'iyyar LP ya zo na uku da kuri'u 22,763, sai kuma 'yan takara 14 da suka fafata a zaɓen waɗanda suka zamu ƙuri'u ƙasa da na manyan ƴan takara uku.

Kara karanta wannan

Zaben kananan hukumomin Kano: Kotu ta dauki mataki kan bukatar jam'iyyar APC

Oshiomhole ya caccaki Gwamnan Edo

A wani rahoton kuma Sanata Adams Oshiomhole ya ce gwamnan jihar Edo mai barin gado, Godwin Obaseki ya mutu murus a siyasance.

Oshiomhole, tsohon gwamnan Edo ya ce duk da kalaman Obaseki na a mutu ko a yi rai, al'umma sun fito sun zaɓi Monday Okpebolo na APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262